Stéphane Pierre (an haife shi a ranar 12 ga watan Oktoban 1981) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Mauritius wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya ga kungiyar kwallon kafa ta Petite Rivière Noire SC a cikin Mauritius League da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Mauritius.[1]

Stéphane Pierre
Rayuwa
Haihuwa Moris, 12 Oktoba 1981 (42 shekaru)
ƙasa Moris
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Petite Rivière Noire SC (en) Fassara2006-
  Mauritius national football team (en) Fassara2007-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya

Sana'a gyara sashe

Pierre ya shafe duka aikinsa yana taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Petite Rivière Noire SC a cikin Mauritian League, farawa a shekarar 2006. Ya lashe Kofin Mauritius tare da PRNSC a shekarar 2007.

Ayyukan kasa da kasa gyara sashe

Pierre ya fara buga wa Mauritius wasa a gasar cin kofin COSAFA a shekarar 2007 da Afirka ta Kudu a matsayin wanda ya maye gurbin.[2] Ya koma buga wasan kwallon kafa na duniya a wasan neman tikitin shiga gasar CHAN na shekarar 2014 a Mauritius da Comoros a shekarar 2012, yana da shekaru 31. A lokacin gasar cin kofin COSAFA na shekarar 2013, Pierre ya zira kwallaye 3 a ragar Mauritius don kammala a matsayin dan wasa na 2 mafi girma a gasar.

Manazarta gyara sashe

  1. Hilary; Gjerde, Arild; Heijmans, Jeroen; Mallon, Bill ; et al. " Stéphane Pierre Olympic Results" . Olympics at Sports-Reference.com . Sports Reference LLC. Archived from the original on 18 April 2020. Retrieved 13 August 2017.
  2. "CORRECTED - Cosafa Cup results" . ESPN. 27 May 2007. Retrieved 22 July 2013.