Sophia wata sakakuwa (mutum mutumi) ce ta dan adam wadda wani kamfani na Hong Kong mai suna Hanson Robotics Limited ya samar. Sophia an kammala gina ta 14 g Fabrairun shekarar 2016,[1] kuma an baiyana ta ne a bainar jama'a be wani kasaitaccen biki da akayi a Austin, Texas kasar Amurika.[2]

Sophia (sakako)
humanoid robot (en) Fassara
Bayanai
Farawa 2016
Ƙasar asali Saudi Arebiya
Ƙasa Sin
Lokacin farawa 19 ga Afirilu, 2015
Manufacturer (en) Fassara Hanson Robotics Limited (en) Fassara
Designed by (en) Fassara David J. Bonda (en) Fassara
Shafin yanar gizo hansonrobotics.com…
Sophia (sakako)
Sophia (sakako)
Sophia a Geneva 2018

Sophia ta kuma baiyana a kafafen sadarwa daban daban a duniya cikin tattaunawa daban daban. A Oktoban shekarar 2017 kasar Saudi Arabiya ta ba Sophi shedar zama yar kasar, abinda yasa Sophia tazama sakako na farko a duniya daya taba samun shaidar dan wata kasa.[3][4] A Nuwamba 2017 ne aka ma Sophia lakabin Shirin cigaban Mahalisar Dinkin Duniya irinta na farko da yayi nasarar wannan take a cikin kirkira wanda ba dan adam ba.[5]

Sophia ta fara aiki ne 14 ga Fabrairun shekarar 2016.[6][7] An kuma sarrafa sakakon ne domin wata tsohuwar sarauniyar Masar Nefertiti,[8] Makirkirin ta David Hanson, yace Sophia tana da kaifin basira ta kwakwalwa, tana da masarrafi na gano da kuma fahimta ta ganeabubuwa. Hakanan Sophia tana jin yanayi irin na dan adam kuma zata iya amsa wasu tambayoyi sannan kuma zata iya yin hira musamman tattaunawar data shafi yanayin muhalli.[9] Sophia tana amfani da masarrafin dake gane furuci na murya daga haruffa, fasaha ce daga kamfanin "Alphabet Inc." da "Google" suka tsara masarrafin domin yazama mai kaifin basira na tsawon lokaci. Tana da wani inji mai taimaka ma furucin ta, hakanan ma yana taimaka mata har take iya yin waka. Amma asalin manhajar basira ta Sophia kamfanin Hansom Robotics ne ya kera shi.[10][11] Shirin AI mai tantancew tattaunawa ne yabata damar mayar da magana.[12]

Hansom ya tsara Sophoa tazama masarrafi mai sauki domin tallafawa a gida da wajen aikin jinya dama a manya manyan tarurruka da wuraren shakatawa. Yace kuma akwai fatan sakako zaiyi hulda da Dan adam cikin yanayi na rayuwa.[3]

Sophia nada wasu yan'uwan ta sakakai wadanda kamfanin na Hansom ya samar dash guda tar.[13] Sauran kere kere na kamfanin na Hansom Robotics sun hada da Alice, Albert Einstein Hubo, BINA48, Han, Jules, Professor Einstein, Philip K. Dick Android, Zeno,[13] da Joey Chaos.[14]

Manazarta

gyara sashe
  1. Mallonee, Laura (March 29, 2018). "Photographing a Robot Isn't Just Point and Shoot]". Wired. Retrieved October 10, 2018.
  2. "Meet Sophia, the female humanoid robot and newest SXSW celebrity". PCWorld (in Turanci). Archived from the original on December 25, 2018. Retrieved January 4, 2018.
  3. 3.0 3.1 "Meet the first-ever robot citizen — a humanoid named Sophia that once said it would 'destroy humans'". Business Insider. October 27, 2017. Archived from the original on October 31, 2017. Retrieved October 28, 2017.
  4. "World's first robot 'citizen' Sophia is calling for women's rights in Saudi Arabia". CNBC (in Turanci). Retrieved May 16, 2018.
  5. "UNDP in Asia and the Pacific Appoints World's First Non-Human Innovation Champion". UNDP Asia and the Pacific. Archived from the original on July 9, 2018. Retrieved July 21, 2018.
  6. "Photographing a robot isn't just point and shoot". Wired. March 29, 2018.
  7. "Hanson Robotics Sophia". Hanson Robotics.
  8. "David Hanson Interview". The Ethics Incubator. Retrieved Jan 28, 2020. Cite has empty unknown parameter: |1= (help)
  9. "Hanson Robotics in the news". Hanson Robotics.
  10. "Beh Goertzel: How Sophia the robot works". aNewDomain. June 1, 2018. Retrieved October 10, 2018.
  11. "I met Sophia, the world's first robot citizen, and the way it said goodbye nearly broke my heart". Business Insider. October 29, 2017. Archived from the original on November 5, 2017. Retrieved October 30, 2017.
  12. "Charlie Rose interviews ... a robot?". CBS 60 Minutes. June 25, 2017. Retrieved October 28, 2017.
  13. 13.0 13.1 "The first-ever robot citizen has 7 humanoid 'siblings' — here's what they look like". Business Insider (in Turanci). Retrieved January 4, 2018.
  14. White, Charlie. "Joey the Rocker Robot, More Conscious Than Some Humans". Gizmodo (in Turanci). Archived from the original on December 22, 2017. Retrieved January 4, 2018.