Martin Škrtel (an haifeshi a ranar 15 ga watan Disamban, 1984), tsohon dan wasan Slovak ne kuma kwararren dan wasa wanda yake taka leda a matsayin dan wasan baya.

Skrtel
Rayuwa
Haihuwa Handlová (en) Fassara, 15 Disamba 1984 (39 shekaru)
ƙasa Slofakiya
Karatu
Harsuna Slovak (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
FC Baník Prievidza (en) Fassara1990-2001
  FK AS Trenčín (en) Fassara2001-2004448
  Slovakia national association football team (en) Fassara2004-
  FC Zenit Saint Petersburg (en) Fassara2004-2008743
  Liverpool F.C.2008-201623916
Fenerbahçe Istanbul (en) Fassara2016-
 
Muƙami ko ƙwarewa centre-back (en) Fassara
Lamban wasa 37
Nauyi 83 kg
Tsayi 191 cm
IMDb nm5080681
martin-skrtel.com

Dan wasan a baya ya buga ma kungiyar kwallon kafa ta FK AS trencin da zenit saint Petersburg kafin ya koma kungiyar kwallon kafa ta Liverpool akan jumillar kudi £6 million a watan Junairu shekara ta alif dubu biyu da takwas 2008. Bayan shekara takwas da rabi daya shafe da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, dan wasan ya buga wasanni har guda dari uku da ashirin 320 inda ya zura kwallo a raga har sau goma sha takwas 18. Ya jona kungiyar kwallon kafa ta Fernebahce har yaci gasar Premier ta kasar Rasha da kuma kofin lig. Haka zalika an zabi dan wasan a matsayin fitaccen dan wasa na Slovak sau hudu.

Dan wasan ya fara buga wasa a Slovak din a shekarar alif dubu biyu da hudu 2004 inda ya buga wasanni guda dari da hudu 104. Inda yazama dan wasa na ukku da yafi Kowane Dan wasa buga wasanni a kasar Slovak kafin ya ajiye a shekarar alif dubu biyu da goma sha tara inda yake bima fitaccen dan wasa mai suna Marek Hamsik da Kuma Miroslav karhan. Ya ajiya kwallo a kasa inda ya shiga jerin mutum goma da suka fi kowa zura kwallo a raga inda yaci kwallaye guda 6.

Dan wasan ya wakilci kasar tashi ta Slovak a gasar kofin duniya na shekarar alif dubu biyu da goma sha hudu 2014 da kuma gasar Euro wadda aka buga a shekarar alif dubu biyu da goma sha shida 2016.

Farkon Rayuwa

gyara sashe

An haifi Skrtl a ranar 15 Disemban 1984 a Handlová.[1]

Rayuwar kwallo

gyara sashe

FC Baník Prievidza and FK AS Trenčín

Skrtel ya fara buga wasa a matsayin kwararren dan wasa a kungiyar kwallon kafa ta FC Baník Prievidza and FK AS Trenčín.

Daga baya kuma sai ya samu nasarar komawa kungiyar kwallon kafa ta FK AS Trencin inda ya samu nasarar buga wasanni guda arba'in da hudu kuma ya samu nasarar jefa kwallaye har guda takwas 8 a tsakanin shekara ta alif dubu biyu 2000 zuwa shekara ta alif dubu biyu da hudu 2004.[2]

Zenit Saint Petersburg

Dan wasan yafa buga wasa a kungiyar kwallon kafar ta zenit saint Petersburg a gasar kofin Rasha wasan da aka buga a ranar 31 Juli shekara ta alif dubu biyu da hudu 2004. A yanda dan wasan ya fada, yace zuwan yan wasan Slovak da kuma zchech shiya sa ya saba da sabuwar kungiyar tashi. Ya buga wasanni har guda dari da goma sha daya 113 inda ya samu nasarar jefa kwallaye har guda biyar 5 kuma ya taimaka ma kungiyar tashi inda ta samu nasarar lashe gasar Premier ta rasha a shekarar alif dubu biyu da bakwai.

Kungiyoyi da yawan gaske sun nuna sha'awar su ga dan wasan

Manazarta

gyara sashe
  1. Samfuri:Cite Aweb
  2. Официальный сайт ФК "Зенит" / Мартин Шкртел (in Rashanci). FC Zenit Saint Petersburg. Archived from the original on 16 October 2007. Retrieved 28 January 2008. Начал заниматься футболом с 6 лет. Воспитанник ФК «Превизда». ... Выступал за юношескую и молодёжную сборные Словакии. ... Карьера игрока. 2001–2004 : ФК «Тренчин», Словакия (45 матчей).