Shehu
Shehu kalma ce da aka samo ta daga larabci (شيخ) kuma ana amfani da ita ne ga mutumin da take da ilimi na addinin mai yawa.
![]() | |
Iri |
taken girmamawa de Islamic cleric (en) ![]() prefix (en) ![]() |
---|---|
Addini | Musulunci |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
![]() |
- Sheik (shehu) tana nufin babban malami wanda yake da matukar sani a fannikan ilimi daban-daban
- Ma'anarta a wajen sufaye tana nufin duk mutumin da iliminsa ya kai a yi masa tambayoyi guda dubu kuma yabada amsar su a take.
Ma'anar ta da larabci
- Tana nufin mutum wanda yake da yawan shekaru.
- Tana nufin mutum wanda yake jagorancin wani addini.
- mutum da yake da girma a wata ƙabila
- mutum da yake jagorancin wata ƙabila
- Tana nufin Mutun mai yawan shekaru musamman ma daga shekara hamsin zuwa shekara tamanin
Anyiwa mutane da yawa lakabi da kalmar shehu a kasar Hausa suna da yawa, wanda suke manyan masana da manyan malamai da manyan mutane a kasar Hausa da wasu sassa na duniya.
Daga cikin na kasar Hausa suna da shehu Usman dan Fodio wanda aka fi sani da mujaddadi, Kuma ana yiwa mafiyan yaron da aka sa masa sunan shehu usman wato Usman da shehu domin girmamawa a gare shi da nuna kimar sunansa da alfarmar da yake da ita wajen musulmai musanman ma mutanen arewacin Najeriya da kuma mutanen Nijer.
Wasu daga cikin shehunnaiGyara
- Shehu Usman dan Fodio
- Shehu Atiku Salga
- Shehu Abdurrahman Suyudi
- Shehu Abdulkadir Jilani
- Shehu Ahmadu Tijjani
- Shehu Nasiru Kabara
- Shehu Ibrahim Inyas
- Shehu Abdullahi fodio (Gwandu)