Selma Elloumi Rekik
Selma Elloumi Rekik ( Larabci: سلمى اللومي الرقيق ; an haife ta a ranar 5 ga watan Yunin shekarar 1956) asalin ta mutuniyar kasar Tunis ce. Ita 'yar kasuwa ce, kuma har wayau yar siyasa ce a ƙasar Tunusiya kuma memba ce ta Nidaa Tounes, duk da cewa a halin yanzu tana cikin kungiyar Al Amal .
Selma Elloumi Rekik | |||||
---|---|---|---|---|---|
6 ga Faburairu, 2015 - 14 Nuwamba, 2018
2 Disamba 2014 - 20 ga Faburairu, 2015 - Lamia Gharbi (en) → District: Q16670949 Election: 2014 Tunisian parliamentary election (en) | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Tunis, 5 ga Yuni, 1956 (68 shekaru) | ||||
ƙasa | Tunisiya | ||||
Ƴan uwa | |||||
Yara |
view
| ||||
Karatu | |||||
Makaranta | Tunis University (en) | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan kasuwa da ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa |
Call for Tunisia (en) Al Amal (en) |
Tarihin rayuwa
gyara sasheElloumi ya kasance memba na kwamitin zartarwa na Nidaa Tounes .
Ta kuma kasance 'yar takarar zaben majalisar dokoki a shekarar 2014 wakiltar jam'iyyarta kuma ta zabi mataimaki a Majalisar wakilan mutane a gundumar farko ta Nabeul.
A ranar 2 ga watan Fabrairun shekarata 2015, an tsayar da ita a mukamin na Ministan Horar da Ma’aikatu da Aiki, [1] sannan aka dauke ta aiki a matsayin Ministar Yawon Bude Ido da kere kere [2] a madadin Amel Karboul, a gwamnatin Habib Essid.
A ranar 13 ga Agustan shekarar 2017, yayin bikin ranar mata, an kuma kawata ta da tambarin Kwamandan Umurnin Jamhuriyar Tunusiya.
A ranar 1 ga Nuwamban shekarata 2018, an naɗa ta darekta a majalisar ministocin shugaban kasa don maye gurbin Selim Azzabi . Ta yi murabus ne a ranar 14 ga Mayu, 2019 a cikin yanayin rikice-rikicen cikin gida a Nidaa Tounes, wanda ta hau kujerar shugabancin 28 ga Mayu. Duk da haka, ta yi murabus daga ofis a ranar 23 ga Yuni, kuma ta bar jam'iyyar.
A ƙarshen watan Yunin, bayan da tsarin shari'a ya amince da Hafedh Caid Essebsi a matsayin wakilin shari'a na jam'iyyar, Elloumi ya karbi shugabancin Amal Tounes, sabon sunan kungiyar Reform Democratic da aka kafa a 2011, yanke shawara duk da haka an soke shi a ranar 20 ga Yuli. Elloumi sannan ya ɗauki shugaban wata ƙungiya, Al Amal, wanda a da ake kira da National Party of Tunisia. Ta kasance 'yar takara a zaben shugaban kasar Tunusiya na shekarar 2019 na 15 ga Satumba, amma a karshe an kawar da ita a zagayen farko. A ranar 24 ga Satumba, 2019, ta yi kira da a saki Nabil Karoui.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Tekiano (français): Habib Essid annonce les noms des membres du nouveau gouvernement tunisien http://www.tekiano.com/2015/01/23/habib-essid-annonce-les-noms-des-membres-du-nouveau-gouvernement-tunisien-video/
- ↑ Leaders Magazine (français) "Qui est Selma Elloumi Rekik, confirmée ministre du Tourisme?" http://www.leaders.com.tn/article/16197-qui-est-selma-elloumi-rekik-confirmee-ministre-du-tourisme