Sani Mu'azu jarumi ne a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood ya shahara ya daukaka a Shirin fim din tashar Arewa 24 mai suna KWANA CASA'IN, inda ya fito a suna Bawa Mai kada , gwamnan jihar alfawa, har ya zama tsohon gwamnan. Fim din shi ya haskaka shi a idon duniya.yanayin fina finan kasasashen waje ya fito a fina finai da dama a shekara ta alif ɗari tara da casa'in 1990.[1]

Tarihin gyara sashe

Cikakken sunan sa kenan sani mu'azu fitaccen jarumi ne a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood. Haifafffen [[Jihar Filato ne garin Jos, an haife shi a ranar 2 ga watan mayu shekarar 1960. Jarumi ne Kuma furodusa sannan Yana aiki a matsayin media consultant na SOWETO. Fina finan shi na kasar wajen

  • Mister Johnson(directed by Bruce beresford a shekarar 1990)[2]

Karatu gyara sashe

sani yayi karatun jarida ne wato (mass communication) a Jami'ar Jos. Ya cigaba da karatun shi a (Nigerian institute of journalism (NIJ) , Wanda ke garin Lagos sannan Yana da Karatun difloma a bangaren (cinematography ) a makarantar digital film production new York film academy a garin new York a kasar India . sannan shine president na (motion pictures practitioners association of Nigeria ).

Manazarta gyara sashe

  1. https://www.blueprint.ng/i-co-founded-the-first-independent-film-production-coy-in-1990-sani-muazu/
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-31. Retrieved 2023-07-31.