Rose Aziza
Rose Oro Aziza (an haife ta a shekara ta 1956) 'yar Najeriya ce mai ilimi a fannin harsuna. Ita ce Farfesa a fannin Harsuna, Shugabar Sashen yaruka da Harsuna kuma Darakta na Shirin Nazarin Urhobo a Jami'ar Jihar Delta (DELSU). [1]
Rose Aziza | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1956 (67/68 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | linguist (en) da Malami |
Rayuwa
gyara sasheAn haifi Rose Aziza a ranar 11 ga watan Maris 1956. Ta tafi St. Maria Goretti Girls Grammar School a Benin kafin ta karanci Turanci a Jami'ar Ife, ta kammala a shekarar 1976. Ta yi karatun digiri na biyu a fannin harsuna a jami'ar Ibadan daga shekarun 1979 zuwa 1980. Ta yi karatun Diploma a fannin ilimi daga Jami'ar Benin daga shekarun 1987 zuwa 1988. A shekarar 1997 ta samu digirin digirgir (PhD) a fannin ilimin harshe a jami’ar Ibadan. [1]
Aziza ta koyar da Turanci a makarantun sakandare da dama kafin ta shiga Sashen Turanci na Kwalejin Ilimi ta Warri. A shekara ta 1999, ta shiga Sashen yaruka da Harsuna a Jami'ar Jihar Delta, inda ta zama Shugabar Sashen a shekarar 2000. Ta zama Farfesa a 2007. A cikin shekarar 2010 an zaɓe ta shugabar tsangayar fasaha, mace ta farko da aka zaɓa Dean a jami'a. A cikin watan Maris 2015 Aziza ta zama mataimakiyar shugabar DELSU.[1]
Ayyuka
gyara sashe- ed. with E. Nolue Emenanjo) Teaching Nigerian languages: experiences from the delta. :
- (ed. with Tanure Ojaide) The Urhobo language today. Lagos: Malthouse Press Limited, 2007.
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 Sunny Awhefeada, Rose Aziza, The Academic Matriarch, @ 60 Archived 2023-11-03 at the Wayback Machine, The Guardian, 13 March 2016. Accessed 2 August 2020.