Rebecca Taylor ('yar siyasa)
Rebecca Taylor ('yar siyasa) | |||
---|---|---|---|
8 ga Maris, 2012 - 30 ga Yuni, 2014 District: Yorkshire and the Humber (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Todmorden (en) , 10 ga Augusta, 1975 (49 shekaru) | ||
ƙasa | Birtaniya | ||
Harshen uwa | Turanci | ||
Karatu | |||
Makaranta |
University of Leeds (en) University of Kent (en) King's College London (en) | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Wurin aiki | Strasbourg da City of Brussels (en) | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Liberal Democrats (en) |
Rebecca Elizabeth Taylor (an haife ta a ranar 10 ga watan Agusta shekarar 1975 ) mai binciken lafiya ce 'yar Burtaniya kuma 'yar siyasarLiberal Democrat ce, wacce ta wakilci mazabar Yorkshire da Humber a Majalisar Turai tsakanin shekara ta 2012 zuwa shekarar 2014.
Kuruciya da ilimi
gyara sasheAn haifi Taylor a Todmorden, wani gari na kasuwaci dake Upper Calder Valley a Calderdale, Yammacin Yorkshire. Mahaifinta, Michael Taylor, shi ne shugaban kungiyar masu sassaucin ra'ayi a Calderdale Metropolitan Borough Council kuma mahaifiyarta, Elisabeth Wilson, ta kasance 'yar takarar Lib Dem na Halifax a babban zaben shekarar 2010, inda ta zo na uku da kuri'u 8,335 (19.1%).
Taylor tana da BA a fannin yaren Jafananci da Nazarin Gudanarwa (1997) daga Jami'ar Leeds, MA a fanninHarkokin Duniya (2001) daga Jami'ar Kent . Daga nan ta fara aikin binciken manufofin kiwon lafiya kuma ta sami digiri na biyu a Kiwon Lafiyar Jama'a (2012) daga King's College London. [1]
Siyasa
gyara sasheTaylor ta tsaya takara a mazabar majalisar Turai na mazabar Yorkshire da Humber a zaben shekarar 2009. ta zo na uku a jerin 'yan takarar Lib Dem, jam'iyyarta ta samu isassun kuri'u ne kawai don zabar 'yar takara da tazo na farko a jerin, MEP mai ci na llokacin, Diana Wallis. Daga nan Taylor ta tsaya takarar kujerar majalisar wakilai ta Rotherham a babban zaben shekara ta 2010 . Ta zo na uku da kuri'u 5,994 (16%). [2]
A watan Yunin shekarar 2012, an nada Taylor a Majalisar Tarayyar Turai don maye gurbin Diana Wallis, wacce ta yi murabus bayan kusan shekaru 13 tana mulki. An zaba Wallis don maye gurbin mijinta kuma Manajan Sadarwa Stewart Arnold, wacce ta kasance ta biyu a jerin 'yan takarar lib Dem a zaben shekarar 2009, amma ta ki amincewa da nadin bayan matsin lamba daga cikin jam'iyyar saboda korafin son zuciya. . Daga nan Arnold ya koma zuwa jam'iyyar Yorkshire. An nada Taylor, wanda itace tazo na uku a jerin 'yan takarar. Taylor ba ta fito takara fito takara kujeraba a zaben shekarar 2014. A maimakon hakan, ta tsaya takarar majalisar wakilai na Morley da Outwood a babban zaben shekarar 2015, inda ta zo ta hudu da kuri'u 1,426 (3%).