Rawani
Rawani ,Yana daga cikin sutura da Hausawa suke amfani da ita kuma suke girmamawa. Sai dai kuma ba duk bahaushe yake amfani da rawani ba, a kasar Hausa idan kaga mutum da rawani to cikin wadannan mutanen ne, Sarki, dan Sarki ko kuma wanda yake da alaqa da gidan sarauta, ko kuma yanada wata sarautar daban. Bangaren sarauta kenan, idan kuma muka dawo bangaren
rawani | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | headgear (en) |
Malunta misali idan kaga Mutum da rawani to kodai Malami ko Almuhajir (Almajiri). Sai kuma bangaren tsofaffi suma ba'a barsu a baya ba don suma sukanyi amfani da rawani sosai. Wannan shine rukunin mutane uku (3) masu amfani da rawani a kasar (Hausa) sai dai akwai dan kadan masu ra'ayin sa rawani suma suna sashi. Amma wadancan rukunin uku sune asali aka sani da rawani. Sai dai rawanin Malamai daban, haka na sarakuna daban, haka tsofaffi shima daban. Rawanin sarakuna shine yafi ko wane rawani girma don nasu har mai kaho biyu akwai. Sai rawanin Malamai shima yana biye da na Sarakuna, sai na tsofaffi shikam wani lokacin ma zaka gashi dai wani daƙun-daƙun dashi. A takaice Rawani wata sutura ce da ake ado da ita a kasar Hausa wadda mafi yawanci mutum ukun na kasa sunfi amfani da ita. .Sarki .Malamai .Tsofaffi[1]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-06-11. Retrieved 2021-06-11.