Rao Muhammad Ajmal Khan
Rao Muhammad Ajmal Khan ( Urdu: راو محمد اجمل خان ; an haife shi 20 Agusta 1954) ɗan siyasan Pakistan ne wanda ya kasance memba a Majalisar Dokokin Pakistan daga watan Agustan 2018 har zuwa watan Agustan 2023. A baya ya kasance ɗan majalisar tarayya daga shekarar 2002 zuwa shekarar 2007 da kuma daga watan Yunin 2013 zuwa watan Mayun 2018.
Rao Muhammad Ajmal Khan | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
1 ga Yuni, 2013 - District: NA-146 (Okara-IV) (en)
District: NA-143 Okara-III (en) | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | 20 ga Augusta, 1954 (70 shekaru) | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||
Imani | |||||||
Addini | Musulunci | ||||||
Jam'iyar siyasa | Pakistan Muslim League (N) (en) |
A halin yanzu yana aiki a matsayin mataimaki na musamman ga Firayim Minista, tare da matsayin Ministan Jiha [1]
Rayuwar farko
gyara sasheAn haife shi a ranar 20 ga watan Agustan 1954.[2]
Harkar siyasa
gyara sasheAn zaɓe shi a Majalisar Dokokin Pakistan a matsayin ɗan takara mai zaman kansa daga Mazaɓar NA-146 (Okara-IV) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2002 .[3] Ya samu ƙuri'u 62,711 sannan ya doke Rao Muhammad Safdar Khan, ɗan takarar jam'iyyar Pakistan Muslim League (PML-Q).[4]A watan Agustan shekarar 2003, an naɗa shi sakataren harkokin man fetur da albarkatun ƙasa na Majalisar Tarayya.[5]
Ya tsaya takarar kujerar Majalisar Dokoki ta ƙasa a matsayin ɗan takarar PML-Q daga Mazaɓar NA-146 (Okara-IV) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2008 amma bai yi nasara ba. Ya samu ƙuri'u 46,006 sannan ya sha kaye a hannun Manzoor Wattoo . A wannan zaɓen, ya tsaya takarar kujerar majalisar dokokin lardin Punjab a matsayin ɗan takara mai zaman kansa daga Mazaɓar PP-192 (Okara-VIII) amma bai yi nasara ba. Ya samu ƙuri'u 65 sannan ya sha kaye a hannun Malik Ali Abbas Khokhar .[6]
An sake zaɓen shi a Majalisar Dokoki ta Ƙasa a matsayin ɗan takarar Pakistan Muslim League (N) (PML-N) daga Mazaɓar NA-146 (Okara-IV) a babban zaben Pakistan na 2013 .[7][8][9][10][11] Ya samu kuri'u 109,998 sannan ya doke Manzoor Wattoo.[12]A lokacin da yake zama dan majalisar tarayya, ya taba zama sakataren majalisar tarayya mai kula da masana’antu da samarwa.[13]
An sake zaɓen shi a Majalisar Dokoki ta ƙasa a matsayin ɗan takarar PML-N daga Mazaɓar NA-143 (Okara-III) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2018 .[14]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Special Assistant to the Prime Minister, with the status of Minister of State
- ↑ "Detail Information". 19 April 2014. Archived from the original on 19 April 2014. Retrieved 9 July 2017.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
- ↑ "PML(Q) replaces N-League on Punjab throne". DAWN.COM (in Turanci). 12 October 2002. Archived from the original on 7 April 2017. Retrieved 6 April 2017.
- ↑ "2002 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 26 January 2018. Retrieved 12 May 2018.
- ↑ "Parliamentary secretaries allocated portfolios". DAWN.COM (in Turanci). 9 August 2003. Archived from the original on 5 March 2017. Retrieved 23 August 2017.
- ↑ "2008 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 5 January 2018. Retrieved 12 May 2018.
- ↑ "Pakistan General Elections 2013 - Detailed results". DAWN.COM (in Turanci). 12 May 2013. Archived from the original on 3 March 2017. Retrieved 3 March 2017.
- ↑ "PML-N, PTI, JUI-F and AML chiefs win elections". The Nation. Archived from the original on 28 March 2017. Retrieved 5 March 2017.
- ↑ "Dozens of turncoats make it to National Assembly". The Nation. Archived from the original on 6 March 2017. Retrieved 5 March 2017.
- ↑ "Manzoor Wattoo loses in Okara NA-146". DAWN.COM (in Turanci). 11 May 2013. Archived from the original on 6 March 2017. Retrieved 5 March 2017.
- ↑ "A wily politician tries to hang on". DAWN.COM (in Turanci). 27 April 2013. Archived from the original on 6 March 2017. Retrieved 5 March 2017.
- ↑ "2013 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 1 February 2018. Retrieved 12 May 2018.
- ↑ "Eleven projects ongoing to promote industries in Balochistan: Rao Ajmal". 22 October 2014. Archived from the original on 23 August 2017. Retrieved 23 August 2017.
- ↑ "PML (N) Rao Muhammad Ajmal Khan wins NA-143 election". Associated Press Of Pakistan. 27 July 2018. Retrieved 3 August 2018.