Racine Coly
Racine Coly (an haife shi ranar 8 ga watan Disambar shekarar 1995) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne kuma ɗan ƙasar Senegal wanda ya taka leda a ƙarshe a matsayin mai tsaron baya ga ƙungiyar Primeira Liga Estoril.
Racine Coly | |||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Dakar, 8 Disamba 1995 (29 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Senegal | ||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Faransanci | ||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | fullback (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 70 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 185 cm |
Aikin kulob
gyara sasheA ranar 31 ga watan Agustan 2017, Coly ya koma ƙungiyar Nice ta Faransa Ligue 1.[1]
A ranar 26 ga watan Janairun shekarar 2021, Coly ya koma kulob ɗin Amiens na Ligue 2 na Faransa, kan yarjejeniyar aro har zuwa Ƙarshen kakar wasa.[2]
Ya koma kulob ɗin Primeira Liga Estoril a ranar 3 ga watan Yunin 2021.[3]
Ayyukan ƙasa da ƙasa
gyara sasheColy ya buga wasa ɗaya a ƙungiyar ƴan ƙasa da shekaru 20 ta Senegal a gasar cin kofin Afirka na ƴan ƙasa da shekaru 20 a cikin shekarar 2015 a wasan kusa da na ƙarshe da suka doke Mali U20 da ci 2-1 a ranar 19 ga watan Maris ɗin 2015.[4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.nicematin.com/football/racine-coly-signe-5-ans-au-gym-163495
- ↑ https://www.lequipe.fr/Football/Actualites/Transferts-racine-coly-nice-prete-a-amiens/1216536
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-08-10. Retrieved 2023-03-21.
- ↑ https://www.cafonline.com/competitions/
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Racine Coly at Soccerway