Rabi'u Rikadawa
Muhammad Rabi`u Rikadawa Wanda aka fi sani da Rabi'u Rikadawa. (an haife shi a ranar 5 ga watan fabrairun shekara ta alif dari tara da saba'in da biyu 1972) a Kaduna (jiha)[1] fitaccen dan wasan film din hausa ne har ma da na kudancin kasa Najeriya wato Nollywood wanda ya kware a bangarori da dama a masana'antar ta kanywood. Ya yi fina-finai irin su Muqabala,Indon ƙauye, Ahlul Kitabi,Labarina.Shirin Labarin na wani shiri ne mai dogon zango da ake haskawa a Arewa 24,shirin labarina shiri ne da ya karawa Rikadawa shura sosai duba da irin rawa da ya taka a shirin.A yanzu haka shirin Labarina yana daga cikin shirye shirye da aka fi kallo a manhajar Youtube
Rabi'u Rikadawa | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Jarumi |
Tarihi gyara sashe
An haifi Rabiu Rikadawa ne biyr ga watan fabrairu shekakara ta alif dari tara da saba'in da biyu (1972) a Jihar Kaduna da ke a arewacin Nigeria.
Iyali gyara sashe
Yana da mata daya da yara 6 maza hudu mata biyu[2]
Shiga Kanywood gyara sashe
Tauraruwar Rikadawa ta fara haskawa ne a shekarar (2015) [3]
Fina-finai gyara sashe
A cikin fina-finan daya fito akwai kamar su
- Mati da Lado
- Kara'i
- Afra
- Kazamin shiri
- Wata ruga
- Adon gari
- Duniya makaranta
- Risala
- Wuff (Mai dogon zango)
- Labarina (Mai dogon zango)
- Ga fili ga Mai doki
- Baya da gura
- Husna da huzna
Da dai sauran su