Rabi' al-awwal
Rabīʿ al-ʾawwal (Larabci ربيع الأوّل) shi ne wata na uku a watannin shekara na Musulunci. A cikin wannan watan Musulmai da dama kan yi bukukuwan Maulidi (bikin murnar haihuwar annabi Muhammad S.A.W). Musulmai mabiya Sunnah sun hakikance da Ranar 12 ga watan aka haifi Annabi Muhamad (s.a.w), yayinda Shi'a suka hakikance da ranar 17 ne da Asuba aka haife Shi. Annabi bai yi bikin Maulidinsa ba da kansa, sai dai ya yi nuni a Hadisi game da Musulmai su rinka azumi a ranar kowacce Litinin domin ita ce ranar da aka haifeshi. Duka dai Musulmai na girmama wannan watan.[1] {{Stub}
Rabi' al-Awwal | |
---|---|
watan kalanda | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | watan Hijira |
Mabiyi | Safar |
Ta biyo baya | Rabi' al-Thani |
Bukukuwan Mauludi
gyara sasheBabu wani hakikanin tarihi game da ainahin ranar ko kwanan watan da aka haifi Annabi Muhammad (s.a.w) sai dai shi din Annabin ya yi nuni da an haife shi a ranar Litinin ne amma bai taba fadan kwanan watan ba. Amma masu bikin Mauludi na daukar ranar 12 ko 17 a matsayin ranar haihuwar Sa. Inda suke gudanar da bukukuwan a sassa daban daban na kasashe da dama na duniya.[2]
Abubuwan tarihi
gyara sashe- Ranar 1 , 89 B H. Aka rusa daular Granada, daular musulunci ta karshe a Andalus.
- Ranar 8, Rasuwar Imam Hassan Al-Askari, (imamin shi'a yan shabiyu).
- Ranar 9, Idin Shuja.
- Ranar 12, Ranar Maulidi na Sufaye.
- Ranar 13 Rasuwar Bibi Rubab (Matar Hazrat Imam Husain a.s)
- Ranar 17, Yan shi'a na bikin murnar ranar haihuwar Imamin su wato Imam Jafar al-Sadik
- Ranar 18, Haihuwar Ummu Kulthum Yar Sayyadina Aliyu.
- Ranar 26, Rasuwar Abu Dalid dan Abdul Mudallab.
Ranar 26, Rasuwar Khawaja Sirajuddin Nakshbandi (jagoran darikar sufaye ta Nakshbandi).
Manazarta
gyara sashe- ↑ Youssof, R. (1890). Dictionnaire portatif turc-français de la langue usuelle en caractères latins et turcs. Constantinople. p. 479.
- ↑ "المنجد في اللغة - المكتبة الوقفية للكتب المصورة PDF". waqfeya.net.