Suna na nufin laƙabi da akewa yaro/yarinya tun gabanin haihuwa kuma wannan suna kan kasance da mutum har iya rayuwarsa. A al'adance, akan yi bikin raɗin suna a yayin da yaro ya kai kwanaki bakwai a duniya inda ake gudanar da taron biki da yanka (dabba, musamman rago) a ranar,[1][2] sannan kuma akan sanya masu suna dangane da rana ko yanayi da akayi haihuwar.

Raɗin Suna
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na ceremony (en) Fassara
bagaren hausawa masu radin suna

Kafin zuwan addinin Musulunci ƙasar Hausa, idan aka haihu ana raɗa wa abin da aka haifa suna ne ta hanyar la’akari da lokaci ko yanayin da aka yi haihuwar. A mafi yawancin lokuta ire-iren waɗannan sunaye kakanni ne ke sanya su. Yana da muhimmanci kafin a kawo ire-iren waɗannan sunaye, a yi waiwaye don duba yadda Hausawa ke gudanar da taron raɗin suna ga ‘ya’yansu kafin zuwan addinin Musulunci a kasar Hausa.

Mutanen Birchi

gyara sashe

A al’adar kaina-fara, mutanen Birchi waɗanda ke zaune a ƙauyen Goda ta ƙasar Birchi a ƙaramar Hukumar Kurfi ta Jihar Katsina, idan mace ta haihu ba ta da damar fita daga ɗakinta, sai bayan kwanaki arba’in, don kuwa a wurinsu wannan ita ce ranar da ake raɗa wa abin da aka haifa suna. A wannan rana, sai dattawa misalin su goma su taru a gidan da aka yi haihuwar. A lokacin da suka haɗu, sai su sanya a samo kundon kara a tsaga shi biyu, daga nan sai su yi zane iri daban-daban a jikin kowane tsagin na wannan kundon kara kamar irin yadda ake yin tsagen fuska na gargajiya. Idan an gama sai a kira wata tsohuwa daga cikin zuriyarsu, a ba ta waɗannan tsagaggun kundon kara wanda akayi wa tsage ta kai wa mai jegon don ta zaɓi ɗaya. Bayan ta zaɓa sai ta miqa wa wannan tsohuwa wanda ta zaɓa, ita kuma tsohuwar, sai ta kawo wa waɗannan dattawa wanda mai jegon ta zaɓa. A lokacin da suka karɓa, sai su duba zanen da yake jikin wanda mai jegon ta zaɓa, ta wannan hanya ce suke gane sunan abin da aka haifa. Daga nan sai su sanar da wannan tsohuwar sunan da aka raɓa wa wanann jariri, ita kuma sai ta sanar da mai jego wadda ta haifi jariri, amma kuma za su gargaɗi tsohuwar ita da mai jegon da kar su kuskura su gaya wa kowa sunan. Su ma dattawan ba za su sanar da kowa ba, sai ranar da za a yi masa aure ne za a sanar da shi da sauran jama’a sunansa. Daga nan sai kakanni su laqaba masa wani suna na daban wanda za a riqa kiransa da shi kafin zuwan ranar aurensa. (Hira da Sarkin Noma Na-Goda a Gidansa da ke Goda Birchi, a ranar 16/8/1988).

Su kuma Maguzawan da suke zaune a kudancin ƙasar Katsina mafi yawancinsu ba ruwansu da taron suna bayan kwana uku ko huɗu da haihuwa. Abin da suke yi kawai shine, idan mace ta haihu, sai a kawo kaji biyu daga gidan mahaifan mijinta don a yin ƙauri.Daga nan ba a sake yin wani abu sai bayan kwana arba’in. A duk tsawon wannan lokaci ba a yi wa abin da aka haifa suna. A lokacin da aka kwana arba’in, sai a yi wani biki wanda mata ne kawai suke taruwa a wurin wanda ake kira "kantsaki" watau a ci abinci a kuma bayar da gudummuwa ga mai jego. Yadda ake yi shi ne, kowace mace da za ta wurin wannan biki tana tafiya da irin gudummuwar da ta ga ya dace ta ba mai jego. A wurin wannan taron ne ake yanka ɗan akuya a yi abinci a ci, a wannan lokaci ne kafin matan su watse suke tunanin lokacin da aka haifi jaririn, wannan ne zai ba su damar zaɓar irin sunan da suka ga ya dace a raɗa wa wannan jariri. Misali, idan an haife shi a lokacin ana ruwa sosai da damina sai su sanya masa suna 'Anaruwa‛ da sauransu (Ibrahim, 1982: 131-132).

Ga Maguzawan da ke gundumar Kwatarkwashi ta Jihar Zamfara waɗanda ke bautar Magiro a garuruwansu na da ba su da wata tsayayyar rana wadda suke raɗa wa ‘ya’yansu suna. A al’adar waɗannan mutane ba a raɗa wa yaro suna sai lokacin da ake da damar yin sunan ko da kuwa bayan shekaru ne. A wurinsu mutum yana iya haɗa ‘ya’yansa da yawa tun daga na ɗaya ko fiye da ɗaya don ya yi masu suna a rana ɗaya. Wannan dalili kansa a wani lokaci, sai a sami mutum har ya yi aure ba a raɗa masa suna ba, sai dai a yi ta kiran sa da sunan kakanni (Hira da Alhaji Joxi Kwatarkwashi, wadda Farfesa Sa’idu Muhammed Gusau ya yi da shi a cikin shekara ta 1985).

A lokacin da wannan mutum ya sami damar yi wa ɗansa ko ‘ya’yansa suna, sai ya gayyaci ‘yan uwa da abokan arziki, ya sanar da su ranar da za a yi sunan. A wannan rana akan haɗa yaran unguwa ɗaya don yi masu suna, kafin zuwan ranar suna, sai uban kowane yaro ya tanadi abin da zai yanka, wannan ne ya sa ake ɗaukar lokaci don yin shiri. A ranar suna sai jama’ar da aka gayyata su taru a kofar gidan da za a yi sunan. Farkon abin da za a fara yi shi ne, sai a ba jama’ar da suka halarta abinci kowa ya ci, a kuma sha giya. Bayan an gama, sai a yanka dabbar suna a feɗe ta a kawo fatar gaban dattawa a ajiye. Daga nan sai babba daga cikin waɗannan dattawa ya kira wanda za a rada wa sunan, sai ya zo gabansa ya durƙusa. Daga nan sai wannan dattijo ya ɗauko fatar dabbar sunan ya rufa ta a kan wanda za a yi wa sunan, ya ce, ‘sunanka wane’, bayan ya raɗa masa suna, sai ya ajiye fatar a wani wuri. Haka za a yi wa dukkan waɗanda za a raɗa wa sunan a wannan rana, ɗaya bayan ɗaya har sai an yi wa kowa (Hira da Alhaji Joxi Kwatarkwashi, wadda Farfesa Sa’idu Muhammed Gusau, ya yi da shi a cikin shekara ta 1985).

Manazarta

gyara sashe
  1. "Yadda Rabe Raben Auren Hausawa Yake A Ƙasar Hausa". www.alummarhausa.com.ng. Retrieved 2023-01-10.
  2. "Suna a Kasar Hausa". www.rumbunilimi.com.ng. Retrieved 2023-01-10.