Paul Glatzel
Paul Milton Glatzel (an haife shi a ranar 20 ga watan Fabrairun shekarar 2001) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne wanda ke buga wa kungiyar Swindon Town, a matsayin ɗan wasan gaba.[1] An haife shi a kasar Ingila, ya kuma wakilci Ingila da Jamus a matakin kwallo na matasa.
Paul Glatzel | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Haihuwa | Liverpool, 20 ga Faburairu, 2001 (23 shekaru) | ||||||||||||||||||
ƙasa |
Jamus Birtaniya | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka |
Farkon rayuwarsa
gyara sasheAn haifi Glatzel a Liverpool, Ingila iyayensa kuma yan asalim Jamus.[2]
Ayyukan kulob dinsa
gyara sasheGlatzel ya fara aikinsa na kwallo tare da Liverpool a matakin kasa da shekara 9. Ya jagoranci tawagar matasa 'yan kasa da shekara 18. Ya sanya hannu kan sabon kwangila na dogon lokaci tare da kulob din a watan Satumbar 2019. Ya rasa kakar 2019-20 saboda rauni, kuma ya ci gaba da samun rauni a watan Satumbar 2020, da Nuwamba 2020. Ya koma aro zuwa Tranmere Rovers a watan Yulin 2021. Glatzel ya fara aikinsa na farko a ranar 7 ga watan Agusta 2021, ya fara ne a nasarar 1-0 a kan Walsall. Ya koma Tranmere a kan aro a ranar 1 ga Satumba 2022. Ya sanya hannu ga kungiyar Swindon Town a ranar 12 ga watan Janairun shekara ta 2024. [3] Ya fara bugawa washegari, ya fara ne a 2-1 a Crewe Alexandra.[4][5]
Ayyukan kasa da kasa
gyara sasheGlatzel ya buga wa Ingila wasa a matakin matasa na kasa da shekaru 15 da kuma na 16, amma ya sauya zuwa Jamus a matakin kasa da shekaru 18.[6] Ya fara buga wasan farko na Jamus na kasa da shekaru 18 a wasan 1-0 da ya ci Cyprus a watan Nuwamba na shekara ta 2018, kuma ya zira kwallaye na farko na matasa na kasa da kasa a wasan 3-0 da ya yi a Belgium a wasan sada zumunci a watan Mayu na shekara ta 2019.[7]
Kididdigar aiki
gyara sasheClub | Season | League | FA Cup | League Cup | Other | Total | ||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Division | Apps | Goals | Apps | Goals | Apps | Goals | Apps | Goals | Apps | Goals | ||
Liverpool | 2020–21 | Premier League | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 1 | 0 | 1 | 0 |
2021–22 | Premier League | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | |
2022–23 | Premier League | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | |
2023–24 | Premier League | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 1 | 1 | 1 | 1 | |
Total | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 2 | 1 | 2 | 1 | ||
Tranmere Rovers (loan) | 2021–22 | League Two | 16 | 4 | 1 | 0 | 1 | 0 | 3 | 2 | 21 | 6 |
Tranmere Rovers (loan) | 2022–23 | League Two | 1 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 1 | 0 |
Swindon Town | 2023–24 | League Two | 19 | 7 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 19 | 7 |
Career total | 36 | 11 | 1 | 0 | 1 | 0 | 5 | 2 | 43 | 14 |
Manazarta
gyara sashe- ↑ Paul Glatzel at Soccerway
- ↑ "Paul Glatzel". Liverpool F.C. Archived from the original on 30 September 2023. Retrieved 18 July 2021.
- ↑ "Swindon sign striker Glatzel and keeper Bycroft" – via www.bbc.co.uk.
- ↑ "Crewe Alexandra 2-1 Swindon Town". BBC Sport (in Turanci). Retrieved 2024-01-13.
- ↑ "Paul Glatzel: Tranmere Rovers re-sign Liverpool forward on season-long loan". BBC Sport. 1 September 2022. Retrieved 1 September 2022.
- ↑ Jones, Neil (6 June 2019). "Liverpool-Talent Paul Glatzel: "German Scouser" mit Comebackqualitäten". Goal.com (in German). Retrieved 9 August 2021.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ "Paul Glatzel". DFB. Retrieved 9 August 2021.