Paul Brannen (an haife shi ranar 13 ga watan Satumba, 1962) ɗan siyasa ne a karkashin Jam'iyyar Labour ne na Biritaniya. Shi tsohon memba ne na Majalisar Tarayyar Turai (MEP) na yankin Arewa maso Gabashin Ingila : an zaɓe shi a 2014 kuma ya rasa kujerarsa a 2019.

Paul Brannen
member of the European Parliament (en) Fassara

1 ga Yuli, 2014 - 1 ga Yuli, 2019
District: North East England (en) Fassara
Election: 2014 European Parliament election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Peterborough (en) Fassara, 13 Satumba 1962 (61 shekaru)
ƙasa Birtaniya
Harshen uwa Turanci
Karatu
Makaranta University of Leeds (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Wurin aiki Strasbourg da City of Brussels (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa Labour Party (en) Fassara

Ƙuruciya gyara sashe

Brannen ya tashi a Tyneside, Arewa maso Gabashin Ingila.[1] Ya halarci Jami'ar Leeds, inda ya karanta tiyoloji da karatun addini. Kasancewa cikin siyasar ɗalibai, ya zama Shugaban Ƙungiyar Jami'ar Leeds.[2] Brannen kuma yana da MBA daga Makarantar Kasuwancin ta Jami'ar Durham.[3]

Sana'ar siyasa da fafutuka gyara sashe

Bayan kammala jami'a, Brannen ya yi aiki da kungiyar Anti-Apartheid Movement, inda ya jagoranci gangamin yaki da kisa daga gwamnatin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu. Ya shahara wajen katse taron manema labarai da Mike Gatting yake yi domin bayyana shirinsa na jagorantar rangadin wasan kurket na 'yan tawaye zuwa kasar Afirka ta Kudu, wanda ya sabawa kauracewa wasannin kasa da kasa. Daga baya ya koma Christian Aid, inda ya jagoranci yakin neman kamfe kan talauci da kuma, kwanan nan, sauyin yanayi. Brannen ya yi shekaru biyar a matsayin Kansila a Majalisar Birnin Newcastle . Sau biyu yana tsayawa takarar dan majalisa ; don Berwick-kan-Tweed a cikin 1997, da na Hexham a 2001. Bai yi nasara ba a zabukan biyu bayan ya zo na biyu.[2][4]

Majalisar Turai gyara sashe

Brannen ya tsaya takara a zaben Majalisar Turai na 2014 a matsayin dan takarar jam'iyyar Labour a yankin Arewa maso Gabashin Ingila.[5] A yayin da jam'iyyar Labour ta lashe mafi yawan kuri'u a yankin, Ya zamo dan majalisar Tarayyar Turai.[6] A ranar 1 ga watan Yuli, 2014, an zaɓe shi a kwamitin noma da raya karkara.[7]

Ya goyi bayan Owen Smith a zaɓen shugabancin jam'iyyar Labour (Birtaniya) a shekarar 2016.[8]

Manazarta gyara sashe

  1. "Paul Brannen - Christian Aid". NEWCASTLE UNIVERSITY INTERNATIONAL DEVELOPMENT CONFERENCE. Newcastle University. 2013. Archived from the original on 27 May 2014. Retrieved 26 May 2014.
  2. 2.0 2.1 "About Paul Brannen". PaulBrannen.co.uk. Archived from the original on 27 May 2014. Retrieved 26 May 2014.
  3. Template:Who's Who
  4. "Paul Brannen: Electoral history and profile". The Guardian. Retrieved 26 May 2014.
  5. "Labour and UKIP claim victory in North East Euro vote". BBC News. Retrieved 26 May 2014.
  6. "North East". Vote 2014. BBC News. Retrieved 26 May 2014.
  7. "Home | MEPs | European Parliament". Europarl.europa.eu. Retrieved 29 October 2021.
  8. Smith, Mikey; Bloom, Dan (20 July 2016). "Which MPs are nominating Owen Smith in the Labour leadership contest?". Mirror.co.uk. Retrieved 10 November 2018.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe