Ouhoumoudou Mahamadou
Ouhoumoudou Mahamadou shekarar (1954-) ɗan siyasan Nijar ne na Jam’iyyar Demokraɗiyya da Gurguzu ta Jamhuriyar Nijar wato (PNDS-Tarayya) wanda kuma yake aiki a matsayin Firayim Ministan Nijar tun daga ranar 3 ga watan Afrilu shekarar 2021 .
Ouhoumoudou Mahamadou | |||||
---|---|---|---|---|---|
3 ga Afirilu, 2021 - 26 ga Yuli, 2023 ← Brigi Rafini
21 ga Afirilu, 2011 - 2 ga Afirilu, 2012 - Gilles Baillet (en) → | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Amaloul Nomade (en) , 1954 (69/70 shekaru) | ||||
ƙasa | Nijar | ||||
Karatu | |||||
Harsuna | Faransanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Nigerien Party for Democracy and Socialism |
Mahamadou ya yi aiki a gwamnatin Nijar a matsayin Ministan Ma'adinai, Makamashi, da Masana'antu daga shekarar 1991 zuwa shekara ta 1993 da kuma Ministan Kuɗi daga watan Afrilun shekarar 2011 zuwa watan Afrilun shekarar 2012. Ya kasance Darakta a majalisar zartarwar shugaban ƙasa tun daga shekarar 2015.
Ayyuka
gyara sasheA cikin gwamnatin riƙon ƙwarya ta Firayim Minista Ahmadou Cheiffou, wanda aka naɗa a ranar 7 ga watan Nuwamban shekarar 1991, Mahamadou ya kasance Ministan Ma'adanai, Makamashi, Masana'antu, da ƙere-ƙere. [1] An ci gaba da rike shi a mukaminsa a cikin garambawul a majalisar zartarwa a ranar 31 ga Janairun 1993. [2] An gudanar da zabubbuka masu yawa a watan Fabrairun shekarar 1993, wanda ya kawo karshen mika mulki; Ba a saka Mahamadou cikin gwamnatin da aka nada a ranar 23 ga watan Afrilu shekarar 1993. [3] Ya yi aiki a matsayin Mataimakin Babban Sakatare na Ƙungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) a karkashin jagorancin Babban Sakatare Édouard Benjamin daga shekarar 1993 har zuwa shekara ta 1998 [4] sannan ya yi aiki a matsayin Wakilin Yankin Taimakon Lutheran na Yankin Afirka ta Yamma. [5]
Bayan da shugaban PNDS Mahamadou Issoufou ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na watan Janairu da watan Maris shekarar 2011 kuma ya hau karagar mulki a matsayin shugaban ƙasar Nijer, an nada Ouhoumoudou Mahamadou a cikin gwamnatin a matsayin Ministan Kudi a ranar 21 ga watan Afrilu shekarar 2011. [6]
Mahamadou ya yi aiki a matsayin Ministan Kuɗi na ƙasa da shekara guda; an kore shi daga gwamnati a ranar 2 ga watan Afrilu shekarar 2012. [7] Daga baya a cikin wannan watan, an nada shi a matsayin Babban Darakta na Banque Internationale pour l'Afrique au Niger (BIA-Niger), babban banki. [8]
An naɗa Mahamadou a matsayin Darakta a majalisar zartarwa ta Shugaban kasa a ranar 4 ga watan Yunin shekara ta 2015. [9] Bayan an rantsar da Issoufou a wa’adi na biyu, ya ci gaba da rike Mahamadou a matsayinsa na Darakta a majalisar zartarwar shugaban kasar a ranar 11 ga watan Afrilu shekarar 2016. [10] [11]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Africa Research Bulletin: Political Series, volumes 28–29 (1991), page 10,336.
- ↑ Marchés tropicaux et méditerranéens, issues 2,460–2,485 (1993), page 356 (in French).
- ↑ Bulletin de l'Afrique noire, issues 1,615–1,659 (1993), page 202 (in French).
- ↑ The Weekly Review (1996), page 25.
- ↑ "Q&A with Mahamadou Ouhoumoudou" Archived 2010-12-19 at the Wayback Machine, Lutheran World Relief, 19 February 2009.
- ↑ "Niger unveils new government", Agence France-Presse, 21 April 2011.
- ↑ Aboubacar Yacouba Barma, "Les raisons d’un si léger remaniement" Archived 2013-06-24 at Archive.today, ActuNiger, 2 April 2012 (in French).
- ↑ Aboubacar Yacouba Barma, "Ouhoumoudou Mahamadou recyclé à la tête de la BIA"[permanent dead link], ActuNiger, 30 April 2012 (in French).
- ↑ Aboubacar Yacouba Barma, "Remaniement technique du gouvernement : Jeu de chaises musicales au PNDS", ActuNiger, 4 June 2015 (in French).
- ↑ "Composition du gouvernement de la République du Niger : La Renaissance « acte 2 » en marche", ActuNiger, 11 April 2016 (in French).
- ↑ Boureima Balima (April 4, 2021), Niger's President Bazoum appoints former minister Mahamadou as PM Reuters.