Oraukwu, Anambra

Gari a Jihar Anambra, Najeriya

Oraukwu gari ne, da ke a jihar Anambra, a ƙasar Najeriya. Ada ana kiransa da Ohaukwu.[1] Garin na ɗaya daga cikin garuruwan da ke ƙaramar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra, kuma yana da nisan kusan kilomita 40 daga gabas da Onitsha tare da tsohon titin gangaren Enugu – Onitsha. Kusan kilomita 20 ne daga kudu maso yammacin ƙaramar hukumar Awka.

Oraukwu, Anambra

Wuri
Map
 6°05′N 6°58′E / 6.08°N 6.97°E / 6.08; 6.97
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaAnambra
Labarin ƙasa
Sun raba iyaka da

Mutane gyara sashe

Mazauna Oraukwu sun haɗa da ƴan asalin ƙasar da mazauna sassa daban-daban na ƙasar. Ƴan asalin ƙasar sun ƙunshi mutane masu ilimi da kuma ’yan kasuwa masu arziqi waɗanda ba su da ilimi, ’yan kasuwa ne na duniya. Al’amuran garin dai na gudana ne a ƙarƙashin wani basaraken gargajiya da gwamnatin jihar ta amince da shi da kuma ƴan majalisar ministocinsa da kuma shuwagabannin ƙungiyar ta gari da mambobin da aka zaɓa bisa ga kundin tsarin mulkin garin. Oraukwu yana da fitattun mutane da yawa waɗanda suka yi fice a fannonin rayuwa daban-daban kamar a fannin Ilimi, Kasuwanci da saka hannun jari, masana'antu da sauransu. Sun shahara wajen bunƙasa jarin dan Adam da kuma ci gaban ababen more rayuwa da yawa a bayyane wadanda ƴan asalin ƙasar ke ɗaukar nauyin kansu.

Manazarta gyara sashe

  1. "Cybo". Cybo (in Turanci). Retrieved 2020-05-27.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe