Oliver Batali Albino (11 Nuwamba 1935 - 4 Janairu 2020) ɗan siyasan Sudan ta Kudu ne, ma'aikacin gwamnati kuma marubuci. An haifeshi a Yei . Ya yi aiki a matsayin Ministan Gidaje da Jama'a daga 1975 zuwa 1978 da kuma Ministan ƙwadago a 1985. A watan Yulin 2011, ya zama memba na Majalisar Ƙoli ta Kudancin Sudan.

Oliver Batali Albino
Member of the Council of States of South Sudan (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Yei (en) Fassara, 11 Nuwamba, 1935
ƙasa Sudan ta Kudu
Mutuwa 4 ga Janairu, 2020
Yanayin mutuwa  (Gazawar zuciya)
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Albino a cikin Juba, Yuli 2011

A ranar 4 ga Janairun 2020, Albino ya mutu sakamakon ciwon zuciya a cikin Augusta, Georgia, Amurka. Yana da shekara 84.[1]

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


Manazarta

gyara sashe
  1. "Oliver Albino Obituary". January 2020. Retrieved 11 January 2020.