Nungua
Nungua birni ne, da ke a Gundumar Municipal Krowor a cikin Babban yankin Accra a kudu maso gabashin Ghana kusa da bakin teku.[1] Nungua ita ce wurin zama na goma sha takwas mafi yawan jama'a a Ghana, dangane da yawan jama'ar, da suka kai dubu 84,119.[2]
Nungua | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Ghana | |||
Yankuna na Ghana | Yankin Greater Accra | |||
Gundumomin Ghana | Krowor Municipal District | |||
Babban birnin | ||||
Labarin ƙasa | ||||
Altitude (en) | 28 m |
Siyasa
gyara sasheNungua na cikin mazaɓar Krowor ƙarƙashin jagorancin Agnes Naa Momo Lartey,[3] memba na National Democratic Congress,[4] wanda ya gaji Elizabeth Afoley Quaye na jam'iyyar New Patriotic Party.[5]
Al'adu
gyara sasheMutanen Nungua Ga Adangbes, suna bikin Kpledzoo.[6] Suna cikin dangi takwas, wato: Nii Mantse We, Nii Moi We, Nii Borte We, Nii Adzin We, Nii Borkwei We, Nii Osokrono Mu, Nii Odarteitse Mu, da Nii Djenge Mu. Babban sarkin Nungua shine Sarki (Dr) Odaifio Welentsi III.[7]
Ilimi
gyara sasheAna kuma iya samun damar samun ilimi a kowane matakin karatu a Nungua. Manyan makarantun birnin sun haɗa da:
Makarantun gaba da sakandare
gyara sashe- Jami'ar, Regional Maritime University.[8]
- Lawh Open University College.[9]
- Makarantar Horar da Bankin GCB.[10]
Makarantun Gaba da Firamare
gyara sashe- Makarantar Sakandare ta Nungua.[11]
- Nungua Presbyterian Secondary Commercial School.[12]
- St Peter's Anglican Senior High School.[13]
- Kwalejin Fasaha ta Royal.[14]
Makarantun a matakin farko (na kowa da kowa-public)
gyara sashe- Nungua Methodist '1' Basic School
- Nungua Methodist '2' Basic School
- St. Paul Anglican Basic Schools
- Nungua Lekma Basic Schools
- Nungua Presby Basic Schools.[15]
Sufuri
gyara sasheAna samun damar shiga birnin Nungua ta hanyar layin dogo,[16] hanya/titi[17] da ta teku. Tashar jirgin ƙasan ce ta hanyar sadarwa ta gabas na tsarin layin dogo na ƙasa. An gyara wata gada da ta daina aiki na wani lokaci a shekarar 2009. Taksi, tro tro (karamin bas), Metro Transit Buses suna kan hanya. Mutanen gari kuma suna amfani da kwale-kwale a bakin rairayin teku.[18]
Duba kuma
gyara sashe- Tashoshin jirgin kasa a Ghana
- Elizabeth Afoley Quaye
Manazarta
gyara sashe- ↑ Touring Ghana – Greater Accra Region Archived 11 ga Afirilu, 2012 at the Wayback Machine
- ↑ "World Gazetteer online". World-gazetteer.com. Archived from the original on 30 September 2007.
- ↑ "member of parliament of krowor". 9 December 2020.
- ↑ "National Democratic Congress - Unity, Stability and Development,National Democratic Congress". Archived from the original on 5 September 2021. Retrieved 13 June 2021.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2012-09-17. Retrieved 2023-03-27.
- ↑ "kpledzoo with a difference".
- ↑ "Motivate teachers to give their best — Dr Odaifio Welentsi". Graphic Online (in Turanci). 2017-06-26. Retrieved 2019-10-21.
- ↑ "Regional Maritime University". Regional Maritime University (in Turanci). Archived from the original on 2019-10-21. Retrieved 2019-10-21.
- ↑ "Home - Laweh Laweh Open University Ghana". Laweh (in Turanci). Archived from the original on 2022-02-03. Retrieved 2019-10-21.
- ↑ "GCB Training School Nungua, Greater Accra, Ghana". gh.geoview.info. Retrieved 2019-10-21.
- ↑ "20 Nungua SHS students collapse, rushed to hospital". Citinewsroom - Comprehensive News in Ghana, Current Affairs, Business News, Headlines, Ghana Sports, Entertainment, Politics (in Turanci). 2018-07-03. Retrieved 2019-10-21.
- ↑ "Ghana Telephone Directory : Nungua Presbyterian Secondary Commercial, Accra". www.ghanaweb.com. Retrieved 2019-10-21.
- ↑ "Nungua Donates to St. Peter's Anglican School".
- ↑ "User". Africa Schools Online (in Turanci). 2017-06-07. Retrieved 2019-10-21.[permanent dead link]
- ↑ "schools in Nungua".
- ↑ "Ghana Railway Company starts a two-week free ride". www.myjoyonline.com. Retrieved 2019-10-21.
- ↑ "Akufo-Addo promises interchange at Nungua, dualization of Beach Road". www.ghanaweb.com (in Turanci). Archived from the original on 2019-10-21. Retrieved 2019-10-21.
- ↑ Touring Ghana – Greater Accra Region Archived 11 ga Afirilu, 2012 at the Wayback Machine. touringghana.com.