Erikson Spinola Lima (an haife shi ranar 5 ga watan Yuli 1995), wanda aka fi sani da Nenass, ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Cape Verde, wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya a ƙungiyar AaFK.

Nenass
Rayuwa
Haihuwa Cabo Verde, 5 ga Yuli, 1995 (29 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya

A cikin shekarar 2014, Nenass yayi gwaji a MFF, ƙungiya mafi nasara ta Sweden.[1]

Kafin kakar 2016, ya rattaba hannu kan Vålerenga 2 a cikin rukuni na uku na Norwegian.

A cikin shekarar 2016, ya rattaba hannu a kulob ɗin KFUM Oslo na Norway na matakin na biyu.

A cikin shekarar 2017, Nenass ya rattaba hannu kan Sarpsborg a cikin Top flight Norway, inda ya buga wasan 1 na gasar. [2] A ranar 17 ga watan Satumba 2017, ya yi fara wasan sa na farko a kulob ɗin Sarpsborg yayin rashin nasara daci 0-5 a hannun kulob ɗin TIL. [2]

Kafin kakar 2018, ya sanya hannu a ƙungiyar rukuni na biyu na Norwegian AaFK, ya taimaka musu wajen samun ci gaba zuwa Norwegian Top flight.

Ayyukan kasa da kasa

gyara sashe

Nenass ya fara wasan sa na farko a tawagar kasar Cape Verde daci 2–1 2022 na cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA a kan Liberia a ranar 7 ga watan Oktoba 2021.[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Interview with Nenass" . aafk.no.
  2. 2.0 2.1 Nenass at Soccerway
  3. "Match Report of Liberia vs Cape Verde Islands - 2021-10-07 - WC Qualification" . Global Sports Archive (in Dutch). 2021-10-07. Retrieved 2021-10-07.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe
  • Nenass at Soccerway
  • Nenass at the Norwegian Football Federation (in Norwegian)