Ndegwu

Gari a Jihar Imo, Nijeriya

Ndegwu al'umma ce a ƙaramar hukumar Owerri ta yamma a jihar Imo. Al’ummar ta rabu gida biyar waɗanda suka haɗa da; Umuekerekpu, Umuahum, Umuezu, Umuomara da Umuogwuta. Kowannen kauye yana da ‘yan uwa akalla takwas. Garin Gabas ya yi iyaka da Ndegwu, yamma da Okwukwu, arewa da Amakohia ubi sai kudu da Irete.

Ndegwu

Wuri
Yawan mutane
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Bangare na Owerri ta Yamma
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Addini da Alƙaluma

gyara sashe

Mutanen garin galibinsu Kiristoci ne da mafi yawan su Anglican ne ko Katolika tare da ƴan kiristocin Pentikostal da arna. Mutanen Ndegwu mutane ne masu aiki tuƙuru kuma masu sauƙin zuciya waɗanda suke daraja ilimi. Mutanen dai galibi manoma ne da ’yan kasuwa da ke samun abin dogaro da kai ta wannan hanyar. Ndegwu yana da yanayi mai dacewa wanda ke maraba da masu zuba jari da mutane daga sassan duniya. Akwai makarantun gwamnati guda uku da wasu makarantu masu zaman kansu da ke ba da ilimin matakin farko-(basic) ga al’umma. Haka kuma kasar tana da albarkar ciyayi da ma'adanai musamman danyen mai da aka gano kwanan nan. [ana buƙatar hujja] Wurin yana da albarkar al'adu kuma yana ƙarƙashin jagorancin shugaba janar a matsayin shugaban al'umma. Jihar Imo jiha ce da ke da rinjayen Igbo, inda al'ummar Igbo ke da kashi 98%. [1]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Igbofocus.co.uk". Archived from the original on 2017-10-14. Retrieved 2023-04-30.