Hukumar Yiwa Kasa Hidima (NYSC) wani shiri ne da gwamnatin Najeriya ta kafa a lokacin mulkin soja domin shigar da daliban Najeriya da suka kammala karatu a fannin gina ƙasa da kuma ci gaban ƙasar. Babu aikin soja a Najeriya, amma tun daga shekarar 1973, an buƙaci waɗanda suka kammala karatu a jami'o'i da kwalejin kimiyya da fasaha su shiga shirin bautar ƙasa na tsawon shekara ɗaya.[1] Ana san hakan a matsayin shekarar hidimtawa ƙasa. Ahmadu Ali ya taɓa zama Darakta-Janar na hukumar yiwa kasa hidima wato (NYSC) na farko har zuwa shekara ta 1975.[2] Darakta-Janar mai ci a yanzu shi ne Yusha'u Dogara Ahmed.[3]

Hukumar Yiwa Kasa Hidima

To foster national unity & cohesion
Bayanai
Suna a hukumance
National Youth Service Corps
Gajeren suna NYSC
Iri ma'aikata da government organization (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Mulki
Hedkwata Abuja
Tsari a hukumance government agency (en) Fassara
Tarihi
Ƙirƙira 22 Mayu 1973
Wanda ya samar
nysc.gov.ng
Hedikwatar NYSC ta kasa da ke Abuja
Membobin Corp A Yayin Bikin Rantsuwa A sansanin NYSC Orientation Camp

An naɗa Manjo Janar Suleiman Kazaure a matsayin darakta janar na hukumar yiwa kasa hidima, NYSC a ranar 18 ga Afrilu 2016 kuma ya kasance shugaban na 17 na shirin har zuwa ranar 26 ga watan Afrilun 2019 da aka mayar da shi cibiyar samar da albarkatun ƙasa ta Najeriya.

An kirkiro NYSC ne a ranar 22 ga watan Mayu, 1973 a lokacin mulkin Janar Yakubu Gowon a matsayin hanyar sulhu, sake gina, da sake gina kasa bayan Yaƙin basasar Najeriya. An kafa ta ne bisa doka mai lamba 24, wadda ta bayyana cewa, an ƙirƙiro wannan shiri ne "da nufin karfafawa da bunƙasa alaƙa tsakanin matasan Najeriya da kuma inganta haɗin kan ƙasa".[4]

Ana tura membobin ƙungiyar (masu shiga shirin bautar ƙasa) zuwa jihohin da ba jiharsu ta asali ba, inda ake sa ran za su yi cuɗanya da jama’a kama daga ƙabilu daban-daban, zamantakewa da iyali, su koyi al’adun ’yan asalin wurin da aka kai su. Wannan mataki na kuma nufin samar da haɗin kai a ƙasar da kuma jin daɗin sauran ƙabilu.

Sansanin da ake tura masu gudanar da shirin

gyara sashe

Matasan Najeriya da suka cancanci yin hidimar ana sa ran za su yi rajista a shafin intanet na hukumar NYSC, domin a kira su yin hidima. Bayan rajista, matasan da suka cancanta suna samun wasiƙar kira, wanda ke nuna halin da suke ciki. Lokacin da aka kira su, ana kiran su da "PCMs" Membobin Haɗin Kai.

Ana sa ran membobin da aka baiwa sunan Prospective Corp za su je asalin jihohin da aka tura su don yin hidimar, inda kuma za su idasa rajista da kuma motsa jiki a sansanin, wanda shine kashi na farko-(motsa jikin) na fara karbar horo a shekarar da za suyi hidimar.

Lokacin “wayar da kai” kusan makonni uku ne kuma ana yinsa a cikin “sansanin” da aka keɓe daga dangi da abokai. Akwai sansanonin a jihohi 36 na tarayya Najeriya.[5] A cikin makon farko da ake wayar musu da kai a mabanbanta sansanonin, ana rantsar da PCMs daga nan a ayyana su a matsayin membobin Corps. Hakanan akwai "bikin na gama karbar horo" daga nan a ƙarshen bayan shafe makonni ukkun da ake wayar musu da kai, ana tura membobin ƙungiyar zuwa wurin aikinsu na farko (PPA). Ana sa ran za su yi aiki a matsayin ma'aikata na cikakken lokaci a wuraren da aka tura su na farko-(PPA), sai dai ranar aiki guda ɗaya aka ware don aiwatar da aiki na ci gaban al'umma wanda aka fi sani da CDS. Bayan watanni goma sha ɗaya a PPA ɗin su, membobin ƙungiyar suna ba da izinin hutu na wata ɗaya kafin bikin ƙarewar hidimar na ƙarshe, inda za a ba su satifiket na shaidar kammalawa.[6]

Don samun cancantar shiga cikin masu yinhidimar shekara ɗaya ta tilas, wanda ya kammala karatun dole ne ya kasance ɗan ƙasa ko bai wuce shekaru 30 ba bayan kammala karatunsa, in ba haka ba za a ba shi (Certificate of Exemption), wanda kuma yayi daidai da takardar shaidar sallamar NYSC. Wanda ya gama karatu kafin ya shekara 30 amma ya tsallake shekarar hidimar zai ci gaba da cancanta tunda lokacin da ya kammala karatunsa bai cika shekara 30 da haihuwa ba. NYSC ya zama tilas ta yadda waɗanda suka kammala karatunsu a kasar nan ba za su iya neman a kebe su da kansu sai dai idan sun kasance nakasassu, sun yi aikin soja sama da shekara ɗaya ko kuma sun haura 30 a lokacin da suka kammala. Masu digiri na ɗan lokaci (CEP) ana keɓe su tunda ba a ba su damar yin hidimar ba.[7]

Abubuwan da ake buƙata don yin rijista

gyara sashe

Ya kamata membobin ƙungiyar masu neman yin hidimar su sami ingantaccen adireshin imel mai aiki da lambar wayar Najeriya (GSM) don yin rajista. Hakanan ana buƙatar lambar JAMB da lambar Admishan-(matric number/reg. number) su ga waɗanda suka kammala karatunsu na gida a Nijeriya. Waɗanda su kayi karatu a ƙasashen waje kuma su tabbatar da cewa an amince da cibiyoyin da sukayi karatunsu na kasashen wajen. Hakanan, idan sun yi karatu a ƙasashen da ba na turawa ba, ana sa ran za su fassara abinda ke cikin satifiket naharshen Ingilishi kafin su bayar da satifiket ɗin ga hukumar-(NYSC) domin tantancewa. Hakanan yana da mahimmanci a lura cewa ba a ba da izinin yin rajista ta hanyar wakilai ba saboda kowane ɗan takara za a buƙaci ya yi gwajin (biometric screening).[8]

Waɗanda suka kammala karatun digiri a Najeriya ba su cancanci yin aiki a cibiyoyin gwamnati (da mafi yawan wasu cibiyoyi masu zaman kansu ba) har sai sun kammala hidimar shekara guda ta tilas ko kuma sun sami abin da aka keɓe masu da ya dace da kamar sun yi aikin hidimar. Wadanda suka kammala karatun digirin da aka kebe daga hidimar sun haɗa da waɗanda suka haura shekaru talatin da haihuwa da waɗanda ke da lalurar naƙasa. A cikin shekarar hidima, membobin Corps za su iya samun sabbin ƙwarewa kuma su koyi al'adun jihar da suke aiki a ciki.

Manufofin Shirin

gyara sashe

An lissafta manufofin shirin bautar ƙasa na ƙasa a cikin doka mai lamba 51 na 16 ga Yuni 1993 kamar haka:

  • Don cusa tarbiya a tsakanin matasan Najeriya ta hanyar sanya musu al'adar masana'antu a wurin aiki da kuma sadaukar da kai da biyayya ga Najeriya a duk halin da suka samu kansu.
  • Don daga darajar matasan Najeriya ta hanyar ba su damar koyo game da manyan manufofin ci gaban ƙasa, inganta zamantakewa da al'adu.
  • Don haɓaka a cikin matasan Najeriya halayen tunanin da aka samu ta hanyar gogewa tare da horon da ya dace. Wanda hakan zai sa su kasance masu dacewa wajen haɗa kai domin amfanin ƙasa
  • Don baiwa matasan Najeriya damar samun abin dogaro da kai ta hanyar karfafa musu gwiwa su bunƙasa sana'o'in dogaro da kai.
  • Don ba da gudummawa ga haɓakar tattalin arzikin ƙasa
  • Don haɓaka alaƙa tsakanin matasan Najeriya da inganta haɗin kan ƙasa da nagarta
  • Don kawar da son zuciya, kawar da jahilci, da kuma tabbatar da irin kamanceceniya da yawa a tsakanin ’yan Najeriya na kowace Ƙabila
  • Don haɓaka fahimtar wanzuwar kamfanoni da makomar al'ummar Nijeriya baki ɗaya.
  • Samar da daidaiton daidaikun membobin ƙungiyar masu yiwa ƙasa hidima tare da yin amfani da kwarewarsu yadda ya kamata a fannin bukatun kasa.
  • Cewa gwargwadon iyawa, ana baiwa matasa ayyukan yi a Jihohin da ba Jihohin da suka fito ba
  • Cewa irin wannan rukunin matasa da aka ba su aiki tare suna wakiltar Najeriya gwargwadon iko
  • Cewa matasan Najeriya sun gamu da salon rayuwar al'umma a sassan Najeriya daban-daban
  • Cewa an kwadaitar da matasan Najeriya da su nisanci ra'ayin addini ta hanyar daidaita bambancin addini
  • Wannan ma’aikacin na hidimar an ƙarfafa shi da ya nemi aiki, a ƙarshen hidimar ƙasa na shekara ɗaya, aikin yi a duk faɗin Najeriya, ta yadda za a inganta zirga-zirgar ma’aikata kyauta.
  • Cewa ana jawo masu daukar ma'aikata wani bangare ta hanyar kwarewarsu da membobin kungiyar sabis don ɗaukar ƙwararrun 'yan Najeriya, cikin shiri da dindindin, ba tare da la'akari da jihohinsu na asali ba.

Shirin ya fuskanci suka daga wani yanki mai yawa na ƙasar da kuma ƙorafe-ƙorafe daga jami'an Corps game da albashinsu.[9] An kashe wasu tsirarun matasa da ke gudanar da shirin NYSC a yankunan da aka tura su saboda rikicin addini, ƙabilanci ko na siyasa.[10][11]

Bayan matsalolin tsaro, da yawa, wasu Samfuri:Su suwa ? sun nuna shakku kan ci gaban da shirin ke da shi, kuma sun yi kira da a gudanar da tattaunawa a kan wannan batu.[12] Dole ne a ɗauki matakan riga-kafi don kauce wa faruwar tashin hankali a nan gaba. Dole ne a kiyaye mutunci da martabar shirin ta hanyar magance batutuwan da aka ambata. Kwanan nan, an yi kira da a soke hukumar NYSC. Honarabul Awaji-Inombek Abiante ne ya ɗauki nauyin wannan kudiri, inda ya lissafta rashin tsaro a ƙasar nan, da kashe-kashen da ake yi wa masu yi wa kasa hidima, da gazawar kamfanoni masu riƙe mambobin ƙungiyar bayan sun yi aiki saboda tabarbarewar tattalin arzikin ƙasa, wasu daga cikin dalilan da ya sa hukumar ta NYSC ya kamata a soke ta.[13] Wannan kira na soke NYSC ya ci karo da ra’ayoyi mabambanta. Yayin da wasu shugabannin da suka shude ke adawa da a soke shi saboda ribar da ya samu ya fi hasarar da ake samu, wasu ‘yan Najeriya na ganin shirin ya yi hasarar amfani da shi don haka ya kamata a yi watsi da shi don kaucewa jefa rayukan ‘yan Najeriya marasa laifi ga rashin tsaro da kuma damuwa na shekara guda da ba dole ba.[14][15]

Manazarta

gyara sashe
  1. Marenin, Otwin (1990). "Implementing Deployment Policies in the National Youth Service Corps of Nigeria". Comparative Political Studies. London: SAGE Publishers. 22 (4): 397–436. doi:10.1177/0010414090022004002. S2CID 154677894.
  2. "A Cup of Tea From Yakubu Gowon". AllAfrica. 22 October 2012. Retrieved 28 December 2015.
  3. "JUST-IN: Buhari Appoints Dogara As New NYSC DG". www.leadership.ng. Retrieved 29 January 2023.
  4. "NYSC - About Scheme". www.nysc.gov.ng. Retrieved 6 June 2018.
  5. "Addresses of NYSC orientation camps in every state in Nigeria". Classgist.
  6. ALAWIYE, Abeeb (2020-03-05). "NYSC DG to passing out corps members: Set up businesses to save yourselves frustration of searching for scarce jobs". International Centre for Investigative Reporting (in Turanci). Retrieved 2021-06-01.
  7. "See wetin Nigeria minister of Youth and Sports tok about NYSC". BBC News Pidgin. 2021-05-25. Retrieved 2021-06-01.
  8. "Requirements for Registration/Mobilsation of Corps Members". NYSC Tales.[permanent dead link]
  9. "Nigeria: 3,283 Corps Members Protest in Kaduna". www.allafrica.com. 4 August 2012. Retrieved 10 August 2019.
  10. "Ex-NYSC members, victims of Suleja bomb blast, accuse Jonathan administration of neglect". premiumtimesng.com. January 22, 2013.
  11. "Post Election Violence in Nigeria | URI". www.uri.org. Retrieved 2021-06-01.
  12. "What's the point of Nigeria's National Youth Service Corp?". TRUE Africa (in Turanci). 2015-10-02. Retrieved 2021-06-01.
  13. Adedapo, Adebiyi (2021-05-25). "Reps To Debate Bill Seeking Scrapping Of NYSC". Leadership News - Nigeria News, Breaking News, Politics and more (in Turanci). Retrieved 2021-06-01.
  14. Timothy, Golu (2021-05-30). "[COLUMN] NYSC Must Not Die". Leadership News - Nigeria News, Breaking News, Politics and more (in Turanci). Retrieved 2021-06-01.
  15. "Pros and Cons: The arguments for and against scrapping NYSC". TheCable (in Turanci). 2021-05-27. Retrieved 2021-06-01.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe