Naka Benue Nigeria
Naka Benue Nigeria hedkwatar karamar hukumar Gwer ta yamma ce a jihar Benue a Najeriya. An san ta a matsayin mafi girman samar da zuma da shinkafa a jihar. Tana da yanki 1,094 km² da yawan jama'a 122,145 a ƙidayar 2006. Tana da gundumomi goma sha biyar da kindreds, Wanda ya fara mulki shine (marigayi) Cif Gendaga Damna, kuma Cif Daniel Ayua Abomtse shine babban mai mulki a yanzu. Shugaban na yanzu (mai canzawa/mai riko) shine Hyacinth Kwegi. Akwai wasu muhimman matsugunai a karamar hukumar baya ga hedikwatar, waɗanda suka hada da; Bunaka, Agagbe, Nagi, Aondoana, Kula, Jimba, Anguhar, Atukpu da Ajigba. Ikyande wata shahararriyar kasuwa ce a karamar hukumar Gwer West. Naka Benue suna daya daga cikin fitattun mutanen da suka kafa garin kuma jikan Asha (Onmbaasha) Ahsa-Tor.
Naka Benue Nigeria |
---|
A watan Afrilun 2018, garin Naka ya shiga cikin makoki lokacin da ake zargin wasu sojoji sun mamaye garin tare da kona gidaje kusan 200 kamar yadda kafafen yada labarai da dama ciki har da BBC suka ruwaito. Hakan ya biyo bayan zargin makiyaya da kashe kimanin mutane 24 a kauyen Mbakyondu da ke karamar hukumar Gwer West. [1][2]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Na Soldiers burn our house -Benue pipo". BBC News Pidgin."Na Soldiers burn our house -Benue pipo". BBC News Pidgin.
- ↑ "Benue government confirms Naka attack, reveals those behind invasion". 19 April 2018.