Nahed Sherif
Nahed Sherif ( Larabci: ناهد شريف ), (1 Janairu 1942 - 7 Afrilu 1981) 'yar wasan kwaikwayo ce ta Masar wacce ta yi fice a fina-finan Masar da na kasar Lebanon a cikin shekarun 1960s da 1970s.
Nahed Sherif | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | سميحة زكي النيال |
Haihuwa | Alexandria, 1 ga Janairu, 1942 |
ƙasa | Misra |
Mutuwa | Kairo, 7 ga Afirilu, 1981 |
Yanayin mutuwa | (ciwon nono) |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama |
Kamal el-Shennawi Hussein Helmy El Mohandes (en) |
Karatu | |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
Muhimman ayyuka |
A Storm of Love Ana wa Banati The Killers (fim na 1971) Q16125961 Q106937969 |
IMDb | nm0792285 |
Farkon Rayuwa da Karatu
gyara sasheAn haifi Samiha ( سميحة زكي النيال ) a Cairo. Ta gudu ta bar makarantar (Lycée Français du Caire) ba tare da ta gama ba.
Aikin fim
gyara sasheDarekta Hussein Helmy El-Mohandess ne ya gano ta kuma ta fara fitowa a fim cikin shekarar 1958.[1] A shekarar 1961, ta auri El-Mohandess kuma ya shirya fina-finai guda biyu yana ba ta matsayin tauraruwa tare da Salah Zulfikar a cikin fim ɗin romance, A Storm of Love, na 1961 da kuma fim ɗin wasan kwaikwayo na shekarar 1961, Me and my Daughters.
Fina-finai
gyara sasheYayin da ta auri El-Shennawy, ta haɗu tare da Salah Zulfikar a karo na uku a cikin Virgo (1970) kuma a karo na huɗu a cikin fim ɗin crime-thriller The Killers (1971), duka fina-finai sun yi fice .
Iyali
gyara sasheAuren ta da El-Mohandess ya ɗauki tsawon lokaci kaɗan kuma daga baya ta auri abokin aikinta Kamal El-Shennawi.
Bayan rabuwa da El-Shennawi, Sherif ta koma Lebanon kuma ta fara fitowa fim dinta na Lebanon mai suna Kuwait Connection wanda akayi a shekarar 1973 ( ذئاب لا تاكل اللحم ) darektan Sami A. Khouri wanda ya yi suna da They lady of the black Moons. Daga baya ta fito a wasu fina-finan kasar Lebanon da dama kuma ta auri ɗan kasar Armeniya-Lebanon Edward Gergian. Ta haɗa da Salah Zulfikar a karo na biyar kuma na karshe a harkar kasuwanci; Desire and Price (1978).
Mutuwa
gyara sasheAn gano tana da ciwon nono a ƙarshen shekarar 1970s, kuma ta mutu a cikin 1981.
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Nahied Sherif a ElCinema
- Nahed Sherif on IMDb
Manazarta
gyara sashe- ↑ http://www.elcinema.com/person/pr1035415/ Nahied Sherif] at ElCinema