An haifi Yarima Mustafa a ranar 20 ga watan Fabrairu, shekara ta 1830 a Alkahira . [1] Shi ne ɗa na uku na Ibrahim Pasha na Masar da matarsa Ulfat Qadin (ya mutu a shekara ta 1865). Ya yi karatu a Makarantar Mishan ta Masar da ke birnin ƙasar Paris. Lokacin da yake dan shekara goma sha ɗaya an yi wa Mustafa kaciya. A ranar 18 ga watan Janairu, shekara ta 1863, Yarima Mustafa ya zama magaji ga ɗan'uwansa Isma'il Pasha amma a ranar 28 ga watan Mayu, shekara ta 1866, Sultan Ottoman Abdülaziz ya canza dokar don maye gurbin ya zama ta hanyar namiji kai tsaye na Khedive mai mulki (mataimakin sarki) maimakon wucewa daga ɗan'uwa zuwa ɗan'uwa. Don nuna rashin amincewa da wannan shawarar, Mustafa Fazl Pasha ya bar kasar Masar zuwa kasar Paris, inda ya jagoranci Matasan Ottomans adawa da Sultan Abdulaziz .

Mustafa Fazıl Pasha
Rayuwa
Haihuwa Kairo, 22 ga Faburairu, 1830
ƙasa Misra
Harshen uwa Egyptian Arabic (en) Fassara
Mutuwa Istanbul, 11 Nuwamba, 1875
Ƴan uwa
Mahaifi Ibrahim Pasha of Egypt
Yara
Yare Muhammad Ali dynasty (en) Fassara
Karatu
Harsuna Larabci
Egyptian Arabic (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Bayan ya rasa matsayinsa na farko a cikin layin maye gurbin Yarima Mustafa an nada shi ministan ilimi a shekara ta 1862, kuma an naɗa shi ministan kudi a shekara ta 1864 zuwa shekara ta 1869, dağa baya kuma an na shi ministan shari'a a shekara ta 1871 har zuwa shekara 1872.

Mustafa Fazıl ya mutu a ranar 2 ga watan Disamba, a shekara ta 1875 a gidansa da ke Vezneciler, <ref name="TDV İslâm Ansiklopedisi">"MUSTAFA FÂZIL PAŞA". TDV İslâm Ansiklopedisi (in Harshen Turkiyya). Retrieved 2020-12-08.

Manazarta

gyara sashe
  1. "MUSTAFA FÂZIL PAŞA". TDV İslâm Ansiklopedisi (in Harshen Turkiyya). Retrieved 2020-12-08.