Muhammadu Kabir Usman
Muhammadu Kabir Usman tsohon sarkin Katsina ne, kuma uba ne ga Sarki mai ci a yanzu wato Sarki Abdulmumini Kabir Usman. Sarki Muhammad Kabir ya zama sarki bayan rasuwan mahaifinsa Sarki Usman Nagoggo kuma yaya ne ga Janar Hassan Usman Katsina[1]
Muhammadu Kabir Usman | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | ga Janairu, 1928 |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | 8 ga Maris, 2008 |
Sana'a | |
Sana'a | Ɗan wasan polo |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Tarihi
gyara sasheAn kuma haifeshi a shekarar 1928 a Katsina yayi karatu a makarantar Midil ta Katsina daga shekarar 1941 zuwa shekarar 1947. Sarki yayi kwas na shekara ɗaya a kwalejin ƴan-sanda na Kaduna, kuma an bashi manaja kofu a shekarar 1951, sannan ya zama muƙamin doka a shekarar 1953. Ya kuma yi kwas na ƴansandan ciki (CID) a Lagos, kuma a shekarar 1957 yaje Ingila ya ƙara yin wani kwas akan ƙanannan hukumomi a Midhurst. Sannan ya halarci cibiyar CID na Landon[1].
Ilimi/Aiki
gyara sasheA shekarar 1959 an naɗa shi Kansikan En’en katsina, mai kula da ƴansanda da kurkuku da samar da ruwa a birane sannan an ƙara naɗa shi shugaban hukumar samar wa birane ruwa da kuma shugabancin ƙugiyar sikaut ta katsina. A shekara ta 1961 ya zama wakilin gaskiya coperation dake zaria, kuma yayi aiki a hukumomin bayar da shawarwari a makarantar, sannan ya zama shugaban club na wasan ƙwallon Gora a katsina a 1961[2].
Alhaji muhammadu Kabir Usman ya samu Muƙamai masu yawa a shekarar 1963. A shekaran aka naɗa shi hakimi watau “Magajin Garin Katsina”. An naɗa shi shugaban ƙwallon ƙafa ta katsina, an zaɓe shi ɗn majalisar ƙwallon kafa ta katsina, an bashi zakaran wasan ƙwallon Doki na shekarar 1963. Kuma an bashi kyautar lambar girma ta sadaukin kwara (OON). A tsakanin 1964-1965 ya zama wakili a hukumar ilimi ta ƙaramar hukumar katsina.[2]
Sarauta
gyara sasheShekarar 1981, shekara ce mai muhimmanci ga tarihin Alhaji Muhammadu Kabir Usman (CON) domin a wannan shekaran ya zama sarki kuma ya gaji mulkinsu na iyaye da kakanni daga mahaifinsa Alhaji Usman Nagoggo, wanda yayi mulki daga shekarar 1944 zuwa shekarar 1981, shekaru 37[3].
Biblio
gyara sashe- Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers.ISBN 978-135-051-2. OCLC 43147940.
- Sani Abubakar Lugga, 1950- (2006). Dikko dynasty : 100 years of the Sullubawa ruling house of Katsina, 1906-2006. Katsina, Nigeria: Lugga Press. ISBN 978-978-2105-20-2. OCLC 137997519.
- Warfare in the Sokoto Caliphate : historical and sociological perspectivesISBN0-521-21069-0OCLC2371710
- The Sokoto Caliphate : history and legacies, 1804-2004. Bobboyi, H., Yakubu, Mahmood. (1st ed ed.). Kaduna, Nigeria: Arewa House. 2006. ISBN 978-135-166-7. OCLC 156890366.
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 Sani Abubakar Lugga, 1950- (2006). Dikko dynasty : 100 years of the Sullubawa ruling house of Katsina, 1906-2006. Katsina, Nigeria: Lugga Press. pp.50. ISBN 978-978-2105-20-2.
- ↑ 2.0 2.1 Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. pp.50-51. ISBN 978-135-051-2.
- ↑ Burji, Badamasi Shu'aibu G., 1968- (1997).Gaskiya nagartar namiji : tarihin rayuwar Janar Hassan Usman Katsina. Kano: Burji Publishers. pp.52. ISBN 978-135-051-2.