Moses Chunga
Moses Chunga (an haife shi a ranar 17 ga watan Oktoba, shekara ta alif ɗari tara da sittin da shida 1965A.c) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Zimbabwe mai ritaya wanda ya taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya ga kungiyar Dynamos, Eendracht Aalst da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Zimbabwe. An haife shi ga iyayensa zuriyar Malawi, amma ya zaɓi ya wakilci ƙasarsa ta haihuwa a matakin duniya. Ana yi masa kallon daya daga cikin manyan 'yan wasan tsakiya na Zimbabwe. [1]
Moses Chunga | |||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Harare, 17 Oktoba 1965 (59 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Zimbabwe | ||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya |
Aikin koyarwa
gyara sasheA shekara ta 2002, bayan da ya yi aiki a Dynamos, an nada shi babban kocin Shabanie Mine.[2]
Chunga ya lashe lambar yabo ta farko na gudanarwa tare da Gunners FC, wanda ya zama zakara a gasar Premier ta Zimbabwe a 2009.[3] Daga baya ya bar Gunners kafin farkon kakar wasa ta gaba kuma ya koma kulob ɗin Harare-gefen Shooting Stars. [4] [5]
A cikin watan watan Yunin 2011, CAPS United ta sanar da cewa Moses Chunga ya bar kungiyar, kwana daya bayan da kungiyarsa ta fitar da kungiyar daga wasan kusa dana karshe na BancABC Sup8r ta Highlanders. [6] An sake nada shi a matsayin koci a Gunners FC makonni kadan bayan haka. [7]
A cikin watan Disamba 2012, Chunga ya sake ziyartar Aalst kuma ya sami karramawa daga tsohon kulob dinsa da kuma Majalisar Birni, an gayyace shi don sanya hannu kan littafin Golden Book of Aalst, babbar girmamawa ta al'umma.[8]
A ranar 11 ga watan Maris, 2015, Chunga ya bar Buffaloes FC.[9]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Vickers, Steve (24 August 2003). "Zimbabwe's missing link" . BBC Sport. Retrieved 19 October 2011.
- ↑ "African Soccer Round-Up" . City Press . South Africa. 8 December 2002. p. 14. Archived from the original on 25 April 2012. Retrieved 20 October 2011.
- ↑ "Gunners crowned Zim champions" . BBC Sport. 22 November 2009. Retrieved 20 October 2011.
- ↑ Chunga quit over salary Archived 2016-03-11 at the Wayback Machine. Newzimbabwe.com.
- ↑ Former Zimbabwe Gunners Coach Moses Chunga Now Leads Shooting Stars. Voanews.com (26 January 2010).
- ↑ Moses Chunga leaves CAPS United Archived 2016-03-03 at the Wayback Machine. Newzimbabwe.com (27 June 2011).
- ↑ CAPS, Gunners match abandoned Archived 2016-03-04 at the Wayback Machine. Newzimbabwe.com (17 July 2011).
- ↑ "The day Moses Chunga cried" . Nehanda Radio. 29 December 2012.
- ↑ "Moses Chunga quits Buffaloes" . NewsDay Zimbabwe . 11 March 2015. Retrieved 23 May 2018.
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Moses Chunga at National-Football-Teams.com