Mohammed Bello El-Rufai
Mohammed Bello El-Rufai (an haife shi a shekarata alif 1990). shi ne wakili na ƙaramar hukumar Kaduna ta arewa. Ya kasance babban ɗa namiji ga tsohon gwamnan jihar Kaduna wato Nasir Ahmad el-Rufai mahaifiyarsa itace Hadiza Isma El-Rufai, marubuciya wanda ta wallafa littafin ta na farko mai suna "Abundance of Scorpiuons".[1]
Mohammed Bello El-Rufai | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 11 ga Janairu, 1988 (36 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Farkon rayuwa
gyara sasheAn haife Muhammad Bello a jihar Kaduna a gidan Malam Nasir El-Rufai.
Karatu
gyara sasheMuhammad Bello ya yi karatunsa a Wheaton college Massachusetts. Inda ya karanta political science,international relations da kuma religious studies.
Ya kuma yi karatu a British school of lome. Har ila yau ya yi karatu a Georgetown university, inda ya karanta public relations/corporate communications.
Siyasa
gyara sasheMuhammad Bello ya kasance mutum ne mai sha'awar siyasa kamar yadda mahifinsa ya bayyana acikin littafinsa. Bello ya yi da mahaifinshi a guraben ayyuka daban daban daga bisani ya zama maitaimaka wa sanatan Kaduna ta tsakiya Uba Sani, sannan ya nemi zama wakili a majalisar tarayya dan wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya. Bello El-Rufai ɗan takarar jam'iyyar APC ya yi nasarar zama wakilin Kaduna ta Arewa a majalisar tarayya da kuri'u 51,052.[2][3]. Yanzu yana zama a majalissar ta Nigeria ta 10 akan kujerar Kaduna ta arewa a Abuja, babban birinin kasar