Mizoram jiha ce, da ke a Arewa maso Gabashin ƙasar Indiya. Tana da yawan fili kimanin kilomita arabba’i 21,081 da yawan jama’a 1,091,014 (in ji ƙidayar shekarar 2011). Jihar tarayyar Indiya ce daga shekara ta 1972. Babban birnin jihar da birnin mafi girman jihar Aizawl ne. P. S. Sreedharan Pillai shi ne gwamnan jihar. Jihar Mizoram tana da iyaka da jihohin uku (Assam, Manipur da Tripura) da ƙasar biyu (Bangladesh da Myanmar).