Melville George Holden (25 ga Agusta 1954 - 31 Janairu 1981) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Scotland wanda ya buga wasan gaba. Ya yi aiki a Ingila da Netherlands, Holden ya buga kusan wasanni 150 a gasar League, inda ya zira kwallaye kusan 50.

Mel Holden
Rayuwa
Haihuwa Dundee (en) Fassara, 25 ga Augusta, 1954
ƙasa Birtaniya
Mutuwa Preston (en) Fassara, 1981
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football manager (en) Fassara
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Preston North End F.C. (en) Fassara1972-19757222
Sunderland A.F.C. (en) Fassara1975-19787323
Blackpool F.C. (en) Fassara1978-197830
PEC Zwolle1978-1979100
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka

An haife shi a Dundee, Holden ya buga wa ƙungiyar matasa ta Preston North End wasa, kuma ya fara wasansa na farko a 1972. Daga baya ya buga wa Sunderland da Blackpool, kafin ya koma Netherlands don yin wasa da PEC Zwolle.[1][2]

Rayuwar gaba da mutuwa

gyara sashe

Holden ya mutu sakamakon cutar neurone a farkon 1981, yana da shekara 26; ciwon ya tilasta masa yin ritaya daga buga wasa shekaru biyu da suka gabata. Bayan mutuwarsa, ɗan wasan Preston Peter Litchfield ya ba da gudummawar £1,000 da ya karɓa don lashe kyautar Man of the Match ga wata ƙungiyar agaji ta neurone.[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Mel Holden profile". Post War English & Scottish Football League A–Z Player's Transfer Database. Retrieved 1 October 2010
  2. "Profile" (in Dutch). Voetbal International. Retrieved 10 April 2013
  3. "An Iron and a White". Preston North End Mad. Retrieved 1 October 2010.