Mary Agard Pocock (an haifeta a ranar talatin da daya 31 ga watan Disamba shekara ta alif 1886 - 10 Yuli 1977) 'yar Afirka ta Kudu ce ƙwararriya ce a fannin ilimin phycology.

Mary Pocock
Rayuwa
Haihuwa Rondebosch (en) Fassara, 31 Disamba 1886
ƙasa Afirka ta kudu
Harshen uwa Turanci
Mutuwa Makhanda (en) Fassara, 20 ga Yuli, 1977
Karatu
Makaranta University of London (en) Fassara
Jami'ar Cape Town
Bedford High School for Girls (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a botanist (en) Fassara, phycologist (en) Fassara, mabudi, botanical illustrator (en) Fassara da Malami
Employers Cheltenham Ladies' College (en) Fassara
Jami'ar Rhodes
Wynberg Girls' High School (en) Fassara
Jami'ar Cape Town
Kyaututtuka

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

An haife ta a Rondebosch a cikin shekarar 1886 'ya ce ga William Pocock da Elizabeth Dacomb, Mary Pocock ta halarci makarantar sakandare ta Bedford da Kwalejin Ladies ta Cheltenham.[1] Daga nan Pocock ta halarci Jami'ar Landan inda ta karanci ilimin kimiyyar halittu, inda ta sami digiri a shekarar 1908. Bayan digirinta Pocock ta koyar a makarantun 'yan mata a London da Cape kafin ta ci gaba da karatunta a shekarar 1919; kammala ƙarin digiri na girmamawa a fannin ilimin botany a Cambridge Ta kasance malama a Jami'ar Rhodes na shekara guda a cikin shekarar 1924, matsayin da ta sake ɗauka lokaci-lokaci yayin aikinta. A cikin shekarar 1925 ta yi tafiya tare da Dorothea Bleek daga Rhodesia zuwa Luanda don tattara tsire-tsire masu furanni waɗanda ta yi karatu a Royal Botanical Gardens, Kew da Gidan Tarihi na Biritaniya bayan dawowarta. Ta Koma zuwa Afirka ta Kudu, Pocock ta zama mai sha'awar algae, ta samu PhD kan batun daga Jami'ar Cape Town tana da shekaru 46. A cikin shekarar 1942 ta kafa herbarium na Jami'ar Rhodes (RUH).[2] Ta yi karatun Volvox musamman.[3] Pocock tare da haɗin gwiwar Marion S. Cave ta zama rukuni na farko don gano adadin chromosomes na algae.[4]

Mawallafiya ce tayi wallafe-wallafe fiye da 30 akan algae, yawancin tsire-tsire kuma ana kiran su bayan Pocock.[1] Ta karɓi Medal Crisp na Linnean Society,[2] kuma ta kasance memba na Linnean Society da Royal Society a Africa ta Kudu.[1]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 E. J. Verwey (1999). New Dictionary of South African Biography, Volume 1. HSRC Press. p. 216. ISBN 0796916489.
  2. 2.0 2.1 Marilyn Bailey Ogilvie; Joy Dorothy Harvey (2000). The Biographical Dictionary of Women in Science: L-Z. Taylor & Francis. p. 1035. ISBN 041592040X.
  3. David Kirk (2005). Volvox: A Search for the Molecular and Genetic Origins of Multicellularity and Cellular Differentiation. Cambridge University Press. p. 14. ISBN 0521019141.
  4. Cave, Marion S.; Pocock, Mary Agard (1951). "Karyological Studies in the Volvocaceae". American Journal of Botany. 38 (10): 800–811. doi:10.2307/2438205. ISSN 0002-9122. JSTOR 2438205.