Mary Mbewe ƴar jarida ce ƴar ƙasar Zambiya. Ita ce babbar editar jaridar Daily Nation, kuma mace ta farko da ta zama shugabar babbar jarida a Zambia. A cikin 2020 Ƙungiyar Mawallafin Labarai ta Duniya ta ba ta lambar yabo ta Mata a Labarai (WIN) Editorial Leadership Award for Africa.[1]

Mary Mbewe
Rayuwa
ƙasa Zambiya
Sana'a
Sana'a newspaper editor (en) Fassara da ɗan jarida
takadda akan mary mbewe

Mwebe ta fara aikin jarida a 1991, tana aiki a Daily Mail ta Zambia. A shekara ta 2000 ta zama babbar editar jaridar Daily Mail, mace ta farko da ta zama babbar edita a Zambia.[2]

A watan Mayu 2017 ta shiga jaridar Daily Nation a matsayin babbar edita.[3]

Mwebe ta kasance memba a Kungiyar 'yan jarida ta Zambia (ZUJ). Ita mamba ce a kungiyar Matan Watsa Labarai ta Zambiya (ZAMWA) da Sashen Zambiya na Cibiyar Yada Labarai ta Kudancin Afirka (MISA).[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. Caroline Wafula (8 September 2020). "Zambian Editor Mary Mbewe Wins Media Leadership Award". Daily Nation. Retrieved 6 March 2021.
  2. Audrey Matitsa (8 September 2020). "Journalist Mary Mbewe named WIN Editorial Leadership Award Laureate". Retrieved 6 March 2021.
  3. 3.0 3.1 "Mary Mbewe Editorial Laureate 2020 for Africa – Wan-Ifra". Indian Printer Publisher. 8 September 2020. Retrieved 6 March 2021.