Martins Ihezuo
Ikenna Martins Ihezuo ɗan siyasan Najeriya ne wanda yanzu haka ya zama ɗan majalisar dokokin jihar Imo. [1] [2]
Martins Ihezuo | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jahar Imo, |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheMartins ya fito daga Eziachi a ƙaramar hukumar Orlu kuma shi ɗan Chief Lolo John Ihezuo ne. Ya samu takardar shedar karatunsa na makarantar sakandaren gwamnati da ke Owerri daga baya ya halarci makarantar Federal Arts and Science, Ondo da Jami'ar Legas don karatun sakandare. Daga baya ya sami digiri na biyu da digiri na uku daga Makarantar Law John F Kennedy a Walnut Creek da Jami'ar Arewacin California. [1]
Aikin siyasa
gyara sasheA shekarar 2019, ya kasance ɗan takarar jam'iyyar Action Alliance kuma ya tsaya takarar majalisar wakilai ta tarayya Orlu, Orsu da Oru East. Bayan zaɓen, ya koma jam'iyyar All Progressive Congress kuma a shekarar 2023 aka zaɓe shi a matsayin ɗan majalisa mai wakiltar Orlu. [1] [3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 "HON. MARTIN IHEZUO". Imo State House of Assembly (in Turanci). Retrieved 2024-12-11. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":0" defined multiple times with different content - ↑ Uwadi, Kenneth. "Imo State: We Say No To Intimidation Of Journalists". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 2024-12-11.
- ↑ "ShineYourEye". www.shineyoureye.org. Retrieved 2024-12-11.