Marinette Yetna
Marinette Ngo Yetna (an haife ta shekarar alif 1965 - 24 ga Mayu 2021) 'yar siyasar Kamaru ce wacce ta yi aiki a matsayin mataimakiya. [1]
Marinette Yetna | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Ngo Yetna Marinette | ||
Haihuwa | Logbadjeck (en) , 10 Disamba 1965 | ||
ƙasa | Kameru | ||
Mutuwa | Douala, 24 Mayu 2021 | ||
Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da deputy (en) | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Cameroon People's Democratic Movement (en) | ||
honorablemarinetteyetna-sm.com |
Rayuwar farko da aiki
gyara sasheAn haifi Ngo Yetna Marinette a ranar 19 ga watan Disamba 1965 a Logbadjeck, wani yanki a cikin sashin Sanaga-Maritime a yankin Littoral na Kamaru. [2] Marinette tana da 'yan'uwa maza da mata biyar. Ta girma a Edea kuma ta yi karatun sakandare a Edea Government High School.
Marinette Yetna 'yar kasuwa ce, wacce ta kafa kuma manajar wani kamfani mai suna Sotrapi Sarl kuma ta mallaki otal ɗin Chez Marinette dake Kribi. [3]
Aikin siyasa
gyara sasheMarinette Yetna memba ce ta CPDM. A shekara ta 2002 aka zaɓe ta a matsayin shugabar kungiyar mata ta jam'iyyar CPDM ta ɓangaren Maritime ta Sanaga kuma ta yi aiki a matsayin kansila na ƙaramar hukumar Edea daga shekarun 2002 zuwa 2007. Ta shiga majalisar ne a shekarar 2013 bayan zaɓen ta a matsayin mataimakiyar sanata a zaɓen majalisar dattawa na shekarar 2013 na ranar 14 ga watan Afrilu 2013.
A cikin shekarar 2020, an zaɓe ta a matsayin mataimakiya a Majalisar Dokoki ta Ƙasa yayin zaɓen shekara ta 2020 na Kamaru. [4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Nécrologie : Marinette Ngo Yetna n'est plus". www.cameroon-tribune.cm.
- ↑ "Décès de Marinette Ngo Yetna : La Sanaga Maritime porte le deuil". 237online (in Faransanci). 2021-05-25. Retrieved 2021-07-03.
- ↑ Lebledparle.com. "L'honorable Marinette Ngo Yetna du RDPC est morte". Le Bled Parle : Actualité Cameroun info - journal Cameroun en ligne (in Faransanci). Retrieved 2021-07-03.
- ↑ "Nécrologie : l'honorable Marinette Yetna, députée du Rdpc pour la Sanaga Maritime est morte". Actu Cameroun (in Faransanci). 2021-05-24. Retrieved 2021-07-03.