Marie-Antoinette Rose
Marie-Antoinette Rose | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 4 ga Yuni, 1975 (49 shekaru) |
ƙasa | Seychelles |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa da ɗan jarida |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | United Seychelles Party (en) |
Marie-Antoinette Rose Masaniyar siyasa ce kuma 'yar jarida. Ta kasance memba ta Majalisar Dokokin Seychelles . Ta yi rajista da jam'iyyar Seychelles People's Progressive Front, kuma an fara zabar ta a Majalisar a shekara ta 2006 bisa daidaito; an sake zabar ta a shekarar 2007.
An fara zabar ta a shekara ta 2006, a matsayin memba na Majalisar Dokoki ta Kasa a cikin wani zabe na jerin jam'iyyun SPPF kuma an sake zabar ta ne a shekara ta 2011 don SPPF, wanda aka sake masa suna Parti Lepep . A halin yanzu ita ce shugabar kungiyar 'yan majalisa ta Parti Lepep kuma ta zamo shugaba mafi rinjaye a majalisa. Har ila yau, memba ce ta Ƙungiyar Majalisar Dokoki ta Commonwealth of Nations kuma memba ne na Kwamitin Gyara da Sabuntawa .