Margaret Fritsch
Margaret Goodin Fritsch (Nuwamba 3, 1899 - Yuni 27, 1993) yar asalin Amurka ce. A cikin shekara na 1923 ta zama mace ta farko da ta kammala digiri a Makarantar Gine-gine ta Jami'ar Oregon kuma a cikin shekara 1926 ta zama mace ta farko da take da lasisi a cikin jihar Oregon . Ta ci gaba da tafiyar da kamfaninta na gine-gine kuma daga ƙarshe ta yi aiki a matsayin mai tsara birni a Alaska .
Margaret Fritsch | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Salem (mul) , 3 Nuwamba, 1899 |
ƙasa | Tarayyar Amurka |
Mazauni |
Oregon Alaska |
Mutuwa | Juneau (en) , 27 ga Yuni, 1993 |
Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (Ciwon huhu) |
Karatu | |
Makaranta | University of Oregon (en) Digiri |
Sana'a | |
Sana'a | Masanin gine-gine da zane |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Fritsch Margaret Goodin a cikin 1899 a Salem, Oregon zuwa Richard Bennet Goodin da Ella Emily Buck. Bayan ta halarci Jami'ar Willamette na tsawon shekara guda, ta shiga Jami'ar Oregon don yin karatun pre-med saboda mahaifinta ya yi imanin cewa mata sun fi dacewa da aikin jinya. A jami'a, Fritsch ta yi abokantaka da daliban da suka yi fice a fannin gine-gine, kuma suka yanke shawarar canza zuwa Makarantar Gine-gine. Ta sauke karatu a cikin shekara 1923, [1] ta zama mace ta farko da ta kammala karatun digiri. [2]
Sana'a
gyara sasheBayan kammala karatunta, Fritsch ta kammala aikin horon shekaru uku a kamfanonin Houghtaling da Dougan, Van Etten & Co. da Morris H. Whitehouse . Ta karɓi lasisin ta don yin aikin gine-gine a cikin 1926, ta zama mace ta farko mai lasisi a Oregon, kuma aikinta na farko da aka ba da izini shine ƙirar gidan sorority Delta Delta Delta a Jami'ar Oregon. A wannan shekarar, an zabe ta sakatariyar Hukumar Binciken Gine-gine ta Jihar Oregon—ta zama mace ta farko da ta rike mukamin—kuma ta rike mukamin har zuwa shekara ta 1956.[1]
Fritsch ta hadu da mijinta, Frederick Fritsch, abokin aikin tane da suke gine-gine, a shekarar 1925 kuma sun yi aure a 1928. Sun koma Philadelphia kuma sun kammala haɗin gwiwa ɗaya, gidan sorority Delta Delta a Jami'ar Pennsylvania a 1929. Sun koma Portland, Oregon a 1930, inda Margaret ta kafa ofishinta bayan shekaru uku. An gano Frederick jim kadan bayan aurensu da wata cuta da ba za ta iya warkewa ba, kuma ya kashe kansa a shekara ta 1934; Margaret ta ɗauki ’yar shekara 11 a cikin shekara ta 1935 don rage kaɗaicinta. [2] [1]
An zaɓi Fritsch a Cibiyar Nazarin Gine-gine ta Amurka a 1935 kuma ta ci gaba da aiki da kamfaninta har zuwa 1940, galibi tana zayyana gidajen zama. Bayan farkon yakin duniya na biyu, ta daina aikin gine-gine saboda rashin aiki kuma ta sami aiki a Hukumar Kula da Gidaje ta Portland. Ta ƙaura cen Dan ci gaba da zuwa Alaska a cikin shekara 1957 kuma ta zama mai tsara birni don Juneau da Douglas ta cigaba da tsare gidaje da birane masu ban mamaki aban garen aikin ta na gine-gine awanan shekarar.
Daga baya rayuwa
gyara sasheFritsch ta yi ritaya a shekarar 1974 kuma ta mutu sakamakon ciwon huhu a watan Juneau a 1993. An binne ta a makabartar River View a Portland.