Mamady Alex Bangré (an haife shi ranar 29 ga watan Yuli, 2001). Ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa ne wanda ke taka leda a matsayin winger/gefe a Kulob din Toulouse na. An haife shi a Faransa, yana buga wa tawagar kasar Burkina Faso wasa.[1]

Mamady Bangré
Rayuwa
Haihuwa Toulouse, 29 ga Yuni, 2001 (22 shekaru)
ƙasa Faransa
Burkina Faso
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya

Aikin kulob/ƙungiya [2] gyara sashe

Bangré ya shiga makarantar matasa ta Toulouse yana ɗan shekara 6. A ranar 10 ga watan Afrilu shekarar 2021, ya sanya hannu kan kwantiragin ƙwararru na farko tare da Toulouse. Ya fara wasansa na farko na gwaninta tare da kungiyar a wasan da suka doke Châteauroux da ci 1-0 a gasar Ligue 2 a ranar 10 ga watan Afrilu shekarar 2021.[3]

Ayyukan kasa gyara sashe

An haife shi a Faransa, Bangré dan asalin Burkinabe ne. Ya yi karo/haɗu da tawagar kasar Burkina Faso a wasan sada zumunci da suka yi rashin nasara a hannun Kosovo da ci 5-0 a ranar 24 ga watan Maris shekarar 2022.[4]

Rayuwa ta sirri gyara sashe

Ɗan'uwan Bangré, Cheikh, ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne wanda kuma ya fito daga makarantar Toulouse.[1]

Girmamawa gyara sashe

Toulouse

  • Ligue 2 : 2021-22

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 Toulouse vs. Châteauroux-17 April 2021 -Soccerway". uk.soccerway.com
  2. Kosovo vs. Burkina Faso-24 March 2022-Soccerway". int.soccerway.com
  3. Kosovo vs. Burkina Faso - 24 March 2022-Soccerway". int.soccerway.com
  4. Kosovo vs. Burkina Faso - 24 March 2022-Soccerway". int.soccerway.com

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe