Mamadou Lamine Danfa[1] (an haife shi ranar 6 ga watan Maris ɗin 2001) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne Kuma ɗan ƙasar Senegal wanda ke taka leda a KF Shkupi.

Mamadou Danfa
Rayuwa
Haihuwa Ziguinchor (en) Fassara, 6 ga Maris, 2001 (23 shekaru)
ƙasa Senegal
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  FC Kolos Kovalivka (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya

Aikin kulob gyara sashe

Danfa ya fara buga ƙwallo ne a ƙasarsa kuma ya samo asali ne daga tsarin wasanni na matasa na Casa Sports.

A cikin watan Maris ɗin 2020 ya sanya hannu kan kwangila tare da kulob ɗin Premier League na Ukraine Kolos Kovalivka.[2] Danfa ya fara buga wasansa na farko a gasar firimiya ta ƙasar Ukraine a ƙungiyar FC Kolos a matsayin ɗan wasan da aka sauya rabin lokaci a wasan da suka sha kashi a gida da FC Shakhtar Donetsk a ranar 14 ga watan Yunin 2020.[3]

Ayyukan ƙasa da ƙasa gyara sashe

Ya shiga cikin tawagar ƙwallon ƙafa ta Senegal ta ƙasa da ƙasa da shekaru 20, inda a cikin shekarar 2019 ya zama ɗan wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afrika na ƴan ƙasa da shekaru 20 . Wannan sakamakon ya baiwa tawagar damar samun cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA U-20 na 2019 a Poland, inda shi ma ya shiga, inda ya kai wasan daf da na kusa da ƙarshe tare da tawagar.[4]

Danfa ya fara buga wa tawagar ƙwallon ƙafa ta Senegal wasa a ranar 3 ga watan Agustan 2019 a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin ƙasashen Afrika (3:0) da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Laberiya.[5]

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe

  • Mamadou Danfa at Soccerway
  • Mamadou Danfa at UAF and archived FFU page (in Ukrainian)

Manazarta gyara sashe