Lindela Ndlovu
Lindela Rowland Ndlovu (ya mutu a ranar 18 ga watan Nuwamba 2015) ƙwararren masanin kimiyyar halittu da sunadarai ne ɗan ƙasar Zimbabwe kuma mataimakin shugabar Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta ƙasa. Har ila yau, ya kasance memba wanda ya kafa Cibiyar Kimiyya ta Zimbabwe kuma ya zama shugaban girmamawa na Cibiyar Nazarin Dabbobi ta Afirka ta Kudu.[1]
Lindela Ndlovu | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 20 century |
ƙasa | Zimbabwe |
Mutuwa | 18 Nuwamba, 2015 |
Sana'a | |
Sana'a | Malami da biochemist (en) |
Ya yi aiki a matsayin Farfesa na Kimiyyar Dabbobi a Jami'ar Limpopo da ke Afirka ta Kudu, kuma tsawon shekaru tara ya kasance shugaban tsangayar aikin gona a jami'ar Zimbabwe.[1] Ya shafe shekaru da dama a Amurka yana karantar kimiyyar dabbobi.[2] Ndlovu ya sami digirin sa na Digiri na uku a shekarar 1985 a Jami'ar Guelph da ke Ontario, Kanada.[3]
A cikin shekarar 1995, Ndlovu ya taimaka wajen fara aikin bincike tare da JD Reed daga Jami'ar Wisconsin a fannin ilimin halittu da sunadarai na proanthocyanidins.[4] A cikin shekarar 2007, ya kasance mai karɓar lambar yabo ta Zinariya don Bincike daga Kwalejin Kimiyyar Dabbobi ta Afirka ta Kudu.[1]
Littattafai
gyara sashe- Lindela Rowland Ndlovu; Joseph Francis (1997). Performance and Nutritional Management of Draught Cattle in Smallholder Farming in Zimbabwe. University of Zimbabwe Publications. ISBN 978-0-908307-62-3.
- Lindela R. Ndlovu (1991). Goat Development in Zimbabwe: Prospects and Constraints. Department of Animal Science, University of Zimbabwe.
Mutuwa
gyara sasheYa mutu ba zato ba tsammani a Gallen House Medical Center, Bulawayo, a ranar 18 ga watan Nuwamba 2015.[2][5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 Frans Swanepoel; Aldo Stroebel; Siboniso Moyo (2010). The Role of Livestock in Developing Communities: Enhancing Multifunctionality. AFRICAN SUN MeDIA. pp. 195–. ISBN 978-0-86886-798-4.
- ↑ 2.0 2.1 "Former Nust Vice Chancellor Prof Ndlovu Dies". Radio VOP. 18 November 2015. Archived from the original on 18 November 2015. Retrieved 19 November 2015.
- ↑ Dissertation Abstracts International: The sciences and engineering, University Microfilms (1986), page 4077.
- ↑ Research Partnerships: Issues and Lessons from Collaborations of Ngos and Agricultural Research Institutions. International Institute of Rural Reconstruction. 1999. ISBN 978-0-942717-73-0.
- ↑ "Ex-NUST Vice Chancellor, Ndlovu dies". ZBC. 18 November 2015. Archived from the original on 20 November 2015. Retrieved 19 November 2015.