Linda McAvan
Linda McAvan OBE (an Haife ta a ranar 2 ga Watan Disamba shekara ta alif dari tara da sittin da biyu 1962) yar siyasa ce ta Burtaniya karkashin jam'iyyar Labour Party, wacce ta kasance 'yar Majalisa a Tarayyar Turai (MEP) a mazabar Yorkshire da Humber daga shekarar 1998, lokacin da aka fara zaɓen ta a zaben fidda gwani bayan Norman West yayi murabus daga kujerar sa. Ta yi aiki har sai da ta yi murabus a ranar 19 ga watan Afrilun shekara ta 2019.[1]
Linda McAvan | |||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
1 ga Yuli, 2014 - 18 ga Afirilu, 2019 - Magid Magid (en) → District: Yorkshire and the Humber (en) Election: 2014 European Parliament election (en)
14 ga Yuli, 2009 - 30 ga Yuni, 2014 District: Yorkshire and the Humber (en) Election: 2009 European Parliament election (en)
20 ga Yuli, 2004 - 13 ga Yuli, 2009 District: Yorkshire and the Humber (en) Election: 2004 European Parliament election (en)
20 ga Yuli, 1999 - 19 ga Yuli, 2004 District: Yorkshire and the Humber (en) Election: 1999 European Parliament election (en)
12 Mayu 1998 - 19 ga Yuli, 1999 District: Yorkshire South (en) | |||||||||||
Rayuwa | |||||||||||
Haihuwa | Bradford (en) , 2 Disamba 1962 (61 shekaru) | ||||||||||
ƙasa | Birtaniya | ||||||||||
Harshen uwa | Turanci | ||||||||||
Karatu | |||||||||||
Makaranta | Heriot-Watt University (en) | ||||||||||
Harsuna | Turanci | ||||||||||
Sana'a | |||||||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||||||
Wurin aiki | Strasbourg da City of Brussels (en) | ||||||||||
Kyaututtuka | |||||||||||
Imani | |||||||||||
Jam'iyar siyasa | Labour Party (en) | ||||||||||
lindamcavanmep.org.uk |
Kafin a zabe ta, McAvan ta fara aiki da Majalisar gundumar Barnsley kuma itace Jami'ar Turai akan Coalfields Community Campaign.
Majalisar Tarayyar Turai
gyara sasheMcAvan ta kasance 'yar Majalisar Tarayyar Turai tun shekarar 1998. Daga shekara ta 2014 zuwa shekarar 2019, ta yi aiki a matsayin shugabar kwamitin raya birane. A cikin wannan matsayi, ta jagoranci (tare da David McAllister ) kungiyar Democracy Support and Election Coordination Group (DEG), wanda ke kula da aikinsa ido na harkokin zaben majalisar. [2]
Baya ga ayyukan kwamitinta, McAvan ta kasance memba ce a Majalisar Haɗin Kan Majalisar Dokokin ACP-EU. Ta kasance shugaban rukunin European Parliament's Fair Trade Working Group kuma tayi aiki a ƙungiyar majalissar Turai akan Yammacin Sahara[3] da kuma Kungiyar Hakkin Yara na Majalisar Turai. [4] Har ila yau, ta kasance mai goyon bayan MEP Heart Group, kungiyar 'yan majalisa da ke da ra'ayin inganta matakan da za su taimaka wajen rage nauyin cututtuka na zuciya (CVD). [5]
Tsakanin shekarar 2002 zuwa shekarar 2003, McAvan ta kasance daya daga cikin wakilai 16 na Majalisar Turai na Yarjejeniyar Makomar Turai, karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Faransa Valéry Giscard d'Estaing.
A cikin shekara ta 2002, an zabe McAvan a matsayin mace mafi nagarta a Turai; ta samu lambar yabo daga tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Ireland ta Arewa Mowlam, wanda ya yaba da kokarinta na shigar da mata a nan gaba a Turai.[6] Daga baya a wannan shekarar, duk da haka, ta yi rashin nasara ga Gary Titley a fafatawar don zabar sabon shugaba na MEPs na Labour na Burtaniya.[7]
Tsakanin shekara ta 2004 zuwa shekarar 2009, McAvan ta yi aiki a matsayin ma'ajin kungiyar gurguzu wato European Parliament's Socialist Group.[8] A watan Yunin shekarar 2007 aka zabe ta mataimakiyar shugabar kungiyar.
Tsakanin shekara 2004 da shekarar 2014, McAvan ta yi aiki a kan Kwamitin Muhalli, Kiwon Lafiyar Jama'a da Tsaron Abinci. A shekara ta 2009, ta tsara rahoton Majalisar Turai game da sa ido kan lafiyar magunguna. [9] Ta kuma zauna a kwamitin wucin gadi kan sauyin yanayi tsakanin shekarar 2007 da shekarar 2009; A wannan matsayi, ta kasance cikin wakilan majalisar wakilai a wajen taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya na shekara ta 2008 a Poznań [10] da kuma taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya na shekara ta 2009 a Copenhagen.[11]
McAvan ta goyi bayan Owen Smith a zaben shugabancin jam'iyyar Labour (Birtaniya) na shekarar 2016.[12]
Membobin Jam'iyyar Labour sun zaɓi McAvan don zama 'yar takarar Labour mai matsayi na gaba [1] don Yorkshire da Humber a zaben Turai na 2009, da kyar ta doke Richard Corbett a matsayin mai nasara. A shekarar 2014, ta sake lashe zaben. Ta tsaya a matsayin MEP a ranar 19 ga watan Afrilu shekara ta 2019.[13]
Rayuwa bayan siyasa
gyara sasheTun barin ta Majalisar Tarayyar Turai, McAvan ta kasance tana aiki a matsayin babban darektan huldar Turai a gidauniyar "European Climate Foundation". [14]
Sauran ayyukan
gyara sashe- National Coal Mining Museum for England, Memba a Kwamitin Gudanarwa
- Sake la'akari da Gudunmawar Turai dangane da Adalci na Duniya (GLOBUS), Memba na Kwamitin Ba da Shawarwari akan Siyasa [15]
Karramawa
gyara sasheAn nada McAvan matsayin "Officer of the Order of the British Empire" (OBE) a kyautar lambar yabo na shekarar 2020 New Year Honours dangane da ayyukan agaji da siyasa. [16]
Rayuwa
gyara sasheMcAvan ta auri Paul Blomfield, dan majalisar Labour na Sheffield Central. Ofishinta a mazabarta na nan a yankin Wath-on-Dearne .
Nassoshi
gyara sashe- ↑ "8th parliamentary term | Linda McAVAN | MEPs | European Parliament".
- ↑ Members of the Democracy Support and Election Coordination Group (DEG) European Parliament
- ↑ Members Archived 8 December 2015 at the Wayback Machine European Parliament Intergroup on Western Sahara.
- ↑ Members of the European Parliament Intergroup on Children's Rights European Parliament.
- ↑ Supporters MEP Heart Group.
- ↑ MEP named EU woman of year European Voice, 7 May 2002.
- ↑ Ambrose Evans-Pritchard (5 September 2002), Labour MEPs pick Left-winger as fifth leader in five years The Daily Telegraph.
- ↑ Véronique Vallières (24 November 2004), EPP-ED denies Christmas gifts cash blunder European Voice.
- ↑ A less green Parliament? European Voice, 4 February 2009.
- ↑ Jennifer Rankin (26 November 2008), MEPs flock to Poznań meeting European Voice.
- ↑ The EP's official delegation to the Copenhagen Conference on Climate Change European Parliament.
- ↑ Smith, Mikey; Bloom, Dan (20 July 2016). "Which MPs are nominating Owen Smith in the Labour leadership contest?". Mirror. Retrieved 10 November2018.
- ↑ "8th parliamentary term | Linda McAVAN | MEPs | European Parliament".
- ↑ Lili Bayer (January 20, 2021), Former British MEPs take on Brussels Bubble Politico Europe.
- ↑ Policy Advisory Board Reconsidering European Contributions to Global Justice (GLOBUS).
- ↑ "No. 62866". The London Gazette (Supplement). 28 December 2019. p. N13.
- Yorkshire & Humber Labor Turai zaben yan takarar 2009 yanar www.labour4yorkshire.eu .