Leïla Ladjimi-Sebaï masaniya a fannin tarihi ne, kuma masaniya a fannin ilimin kimiya na kayan tarihi kuma marubuciya, mawaƙiya, daga Tunisiya. Ita kwararriya ce a tarihin matan zamanin Roman a Arewacin Afirka da tarihin Carthage.[1]

Leila Ladjimi-Sebaï
Rayuwa
ƙasa Tunisiya
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a Masanin tarihi, archaeologist (en) Fassara, epigrapher (en) Fassara, marubuci da maiwaƙe

Leïla Ladjimi Sebaï ta kasance Daraktar Bincike, na Cibiyar Tarihi ta Tunisiya tun daga shekarar 2009, kuma Shugabar Ƙungiyar 'Les amis de Carthage' tun a shekarar 2012.[2][3] Tun lokacin da aka kaddamar da ita a cikin shekarar 2014, ta kasance memba na Hukumar Gudanarwa na MUCEM, Gidan Tarihi na Rum a Marseille. Daga shekarun 2002 zuwa 2010 ta kasance Shugabar ICOM (Tunisia), kuma daga shekarun 2002 zuwa 2005 memba ce ta hukumar gyare-gyare a gidan kayan tarihi na Carthage, inda ta kashe mafi yawan ayyukanta, kuma ita ce ke da alhakin babban tarin labaran Latin. Marubuciya ce kuma mawaƙiya, ta wallafa tarin wakoki na farko, Chams, a cikin shekarar 1991, wanda aka ba ta lambar yabo ta "Grand Prix Tahar Haddad de la Nouvelle" a Tunis.

Leïla Ladjimi Sebaï ta horar da raye-raye na gargajiya kuma ta kasance ɗaliba a makarantar Bolshoi Theatre a Moscow (1965-1967).[4] Rubuce-rubucenta a kan matan Afirka a zamanin Romawa daga tushen almara (La femme en Afrique à l'époque romaine: À partir de la documentation épigraphique) ta sami lambar yabo a shekarar 1977 daga Jami'ar Provence.[5]

Kyaututtuka

gyara sashe

Leïla Ladjimi Sebaï ta sami lambar yabo ta Serge Lancel daga Académie des Inscriptions et Belles Lettres (Institut de France, Paris, 2005), don nazarinta akan Carthage.[6] A cikin watan Oktoba 2010 an ba ta matsayin jami'iyyar Ordre des Arts et des Lettres.[7]

Zaɓaɓɓun Ayyuka

gyara sashe
  • Ladjimi, S. L. (2011). La femme en Afrique à l'époque romaine: À partir de la documentation épigraphique. Tunis: Institut national du patrimoine.
  • Ben, A. Z., Ladjimi, S. L., Musée national de Carthage., & Maʻhad al-Waṭanī lil-Turāth (Tunisia). (2011). Catalogue des inscriptions latines païennes inédites du Musée de Carthage. Rome: École française de Rome.
  • Ladjimi, S. L. (2005). La colline de Byrsa à l'époque romaine: Étude épigraphique et état de la question. Paris: C.E.A.M., Institut d'Art et d'Archéologie.
  • Ladjimi, S. L. (2002). Index général des inscriptions latines païennes de Carthage. Tunis: Institut national du patrimoine.
  • Dietz, S., Ladjimi, S. L., Ben, H. H., & Nationalmuseet (Denmark). (1995). Africa proconsularis: Regional studies in the Segermes Valley of Northern Tunesia. Århus: Distributed by Aarhus University Press.
  • Sebaï, L. L. (1993). Elisha: Quatre chants. Tunis: Or du Temps.
  • Galley, M., Ladjimi, S. L., International Association of Studies on Mediterranean Civilizations., & Maʻhad al-Qawmī lil-Āthār wa-al-Funūn bi-Tūnis. (1985). L'homme méditerranéen et la mer: Actes du troisième Congrès international d'études des cultures de la Méditerranée occidentale, Jerba, avril 1981. Tunis: Editions Salammbô.
  • Ben, AZ, & Ladjimi, SL (1983). Index onomastique des inscriptions latines de la Tunisie. Paris: Editions du Center National de la recherche scientifique.

Manazarta

gyara sashe
  1. "histoire". www.cartaginoiseries.org. Archived from the original on 2016-02-05. Retrieved 2021-03-23.
  2. "Ladjimi Sebaï, Leïla - Persée". www.persee.fr. Retrieved 2021-03-23.
  3. "IDRef".
  4. "Arab Women Writers: A Critical Reference Guide, 1873-1999 - PDF Free Download". epdf.pub (in Turanci). Retrieved 2021-03-23.
  5. LADJIMI SEBAI, L; EUZENNAT, M. (1977). La femme en Afrique à l'époque romaine (à partir de la documentation épigraphique|.
  6. "Lettre d'information n°56" (PDF). ACADÉMIE DES INSCRIPTIONS ET BELLES-LETTRES.
  7. "MUCEM" (PDF). p. 36.