Lehlohonolo Seema (an haife shi ranar 9 ga watan Yuni 1980) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Mosotho mai ritaya wanda ya taka leda a matsayin mai tsaron baya kuma ɗan wasan tsakiya. A halin yanzu shi ne manajan kungiyar kwallon kafa ta Lamontville Golden Arrows a gasar Premier ta Afirka ta Kudu.[1]

Lehlohonolo Seema
Rayuwa
Haihuwa Mafeteng (en) Fassara, 9 ga Yuni, 1980 (44 shekaru)
ƙasa Lesotho
Karatu
Harsuna Turanci
Sesotho (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Kungiyar kwallon kafa ta Lesotho1998-2008232
Bloemfontein Celtic F.C.1998-20061138
Orlando Pirates FC2006-2011631
Mpumalanga Black Aces F.C. (en) Fassara2010-201010
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya

Ya koma tawagar Afirka ta Kudu Bloemfontein Celtic a kakar 1998/99, ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Orlando Pirates a shekarar 2006. Bayan da ya taba zama kyaftin din kulob ɗin Bloemfontein Celtic,[2] ya kasance kyaftin na Orlando Pirates kuma ya yi ritaya daga kulob din a ranar 1 ga watan Yuli 2011. [3]

Ayyukan kasa da kasa

gyara sashe

Tauraron tawagar kasar Lesotho, Seema ne kawai dan wasansu wanda a shekarar 2003 ya buga kwallon kafa a kasashen waje. A shekara ta 2001, ya ci kwallon da ta yi nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida a minti na 87 a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Afrika da Zimbabwe a Bulawayo, wanda ya baiwa Lesotho shahararriyar nasara.[4]

Manazarta

gyara sashe
  1. Lehlohonolo Seema at National-Football- Teams.com
  2. "Lesotho - L. Seema - Profile with news, career statistics and history - Soccerway" .
  3. Jonty, Mark (13 September 2004). "Money does buy happiness" . IOL . Retrieved 22 December 2006.
  4. Nkareng, Matshe (6 December 2006). "Bucs duo in trouble again" . IOL . Retrieved 22 December 2006.