Lazarus Chakwera
Lazarus McCarthy Chakwera (an haife shi ranar 5 ga watan Afrilu shekarar 1955) ɗan siyasan Malawi ne kuma wanda ya yi aiki a matsayin Shugaban Malawi kuma ministan tsaro tun watan Yunin shekarar 2020.[1] Har ila yau, yana aiki a matsayin ministan tsaro ga kundin tsarin mulkin Malawi, Ya yi aiki a matsayin shugaban jam'iyyar Congress Party daga 2013.[2] Ya kasance Shugaban majalisar Cocin (Assemblies of God) a Malawi daga 1989 zuwa 2013.
Lazarus Chakwera | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
28 ga Yuni, 2020 - ← Peter Mutharika (en) Election: 2020 Malawian presidential election (en)
28 ga Yuni, 2020 - 31 ga Janairu, 2023 ← Peter Mutharika (en)
2010 - District: Lilongwe North West (en) Election: Malawian legislative election, 2014 (en) | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | Lilongwe, 5 ga Afirilu, 1955 (69 shekaru) | ||||||
ƙasa | Malawi | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta |
Jami'ar Malawi Jami'ar Limpopo Trinity International University (en) Jami'ar Afirka ta Kudu | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa, Malamin akida da Malami | ||||||
Imani | |||||||
Addini | Assemblies of God (en) | ||||||
Jam'iyar siyasa | Malawi Congress Party (en) |
A baya, Chakwera shi ne shugaban ƴan adawa a majalisar dokokin kasar bayan zaɓukan da aka gudanar a ranar 21 ga watan Mayun shekarar 2019 da kotun tsarin mulkin kasar ta soke. An nada shi shugaban SADC a ranar 17 ga watan Agusta[3] a taron shekara-shekara na SADC karo na 41 da aka gudanar a ranar 9 ga Agusta zuwa 19 ga Agusta 2021 a Lilongwe, Malawi.
Rayuwarsa
gyara sasheAn haifi Lazarus a Lilongwe, babban birnin Malawi, a ranar 5 ga watan Afrilu shekarar 1955 [4] a lokacin da ƙasar ke ƙarƙashin mulkin mallaka na Burtaniya.[5] Mahaifinsa malamin makarantar firamare ne kuma yana samun abin hidima da ciyar da iyalinsa ta hanyar sana'ar noma.[6] Ya auri Monica Chakwera a ranar 8 ga watan Oktoba, shekarar 1977, sun haifa ƴa'ƴa huɗu (namiji ɗaya da mata 3).[7]
Karatu
gyara sasheChakwera ya kammala karatun digiri na farko a sashen Arts (Palsapa) daga Jami'ar Malawi a shekarar 1977. Ya karanta ilimin tauhidi sannan ya sami digirin girmamawa a Jami'ar Arewa ta Afirka ta Kudu sannan ya sami digiri na biyu (MTh) a Jami'ar Afirka ta Kudu a 1991.[7] Jami’ar Trinity International da ke Amurka ta ba shi digirin digirgir (D.Min) a shekarar 2000. Ya zama farfesa a Makarantar Pan-Africa Theological seminary a 2005.[5]
Aikin Tauhidi na coci
gyara sasheYa yi aiki a matsayin malami a (Assemblies of God) daga 1983 zuwa 2000 inda ya zama Shugaban Makarantar a 1996. Ya kasance babban darekta kuma malami a Makarantar Tauhidin kiristanci ta Duniya.[8] Daga 1989 zuwa 2013 ya jagoranci Majalisar Malawi ta Ubangiji.[8] A ranar 14 ga Afrilu 2013 ya ba wa mutane da yawa mamaki lokacin da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a babban taron jam'iyyar adawa ta Malawi Congress Party (MCP) a matsayin shugaban kasa yayin da yake ci gaba da rike Majalisar Dokokin ubangiji.[9]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Lazarus Chakwera sworn in as Malawi president after historic win". BBC News. 28 June 2020. Retrieved 28 June 2020.
- ↑ Welle (www.dw.com), Deutsche. "Who is Malawi's new leader Lazarus Chakwera? | DW | 27.06.2020". DW.COM (in Turanci). Retrieved 2021-01-11.
- ↑ "Southern Africa: SADC to Hold 41st SADC Summit in Malawi". allAfrica.com (in Turanci). 2021-08-09. Retrieved 2021-08-20.
- ↑ "Curriculum Vita: Lazarus M. Chakwera, BA, BTh (Hons), MTh., D.Min" (PDF). Wise One From The East. Archived from the original (PDF) on 5 October 2013.
- ↑ 5.0 5.1 "Man of God, Welcome to Cut Throat Politics". Zodiakmalawi.com. 17 April 2013. Archived from the original on 30 June 2013. Retrieved 3 October 2013.
- ↑ "Personal Story of Lazarus Chakwera : AGTV". Agtv.ag.org. 24 June 2010. Retrieved 3 October 2013.
- ↑ 7.0 7.1 "Malawi on the road to 2014: Rev. Dr. Lazarous Chakwera". Nyasa Times. 15 April 2013. Archived from the original on 4 March 2016. Retrieved 3 October 2013.
- ↑ 8.0 8.1 "On the Road to 2014: Dr. Lazarus McCarthy Chakwera". Malawi Voice. Archived from the original on 4 October 2013. Retrieved 3 October 2013.
- ↑ "Chakwera guns for MCP presidency". Archived from the original on 16 May 2013. Retrieved 22 April 2013.