Lawal Sama'ila Yakawada tsohon ciyaman ne a garin giwa karamar hukumar Giwa, Jihar Kaduna. Kuma tsohon sakataren[1] gwamnatin Jihar Kaduna ne[2]

A lokacin marigayi gwamna Patrick Ibrahim Yakowa. Lawal Yana daga cikin wadanda ake damawa dasu a [3]siyasar gwamnatin jihar kaduna.[4][5][6][7]sannan shine me bama gwamnan jihar shawara a lokacin tsohon gwamnan Malam Nasir Ahmad elrufa I

Lawal ya koyi siyasa ne tun a gida gurin mahaifin sa kasancewar sa Yana mulkar Al,umma. lawal ya zauna tare dashi , sannan ya zauna da mutane da dama inda ya koyi siyasar mutunta mutane da kawo musu cigaba , lawal ya fara zama shugaban Al,umma tun a lokacin da yake karatu a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya, lawal yayi shugabancin karamar hukumar Giwa, Kuma tsohon sakataren gwamnatin jihar Kaduna.

Lawal yayi karatun sa na muhammadiyya a garin su yakawada Karamar hukumar giwa, yayi firamare acan daga Nan yazo kwalejin Sardauna dake Zaria daga Nan ya shiga jami'ar Ahmadu bello Dake Zaria.

Lawal Yana da mata guda biyu hassana wacce itace uwargida, Sai amarya asma,u, suna da Yara da dama dashi.yana da manyan yara.

Manazarta

gyara sashe
  1. https://dailytrust.com/new-boards-of-parastatals-inaugurated/
  2. https://www.premiumtimesng.com/tag/lawal-samaila-yakawada
  3. https://dailynigerian.com/kaduna-apc-welcomes/
  4. https://hausa.legit.ng/1181149-lawal-samaila-yakawada-da-uba-sani-na-neman-zama-sanata-a-kaduna.html
  5. https://thenationonlineng.net/tag/ssg/page/7/
  6. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-17. Retrieved 2023-07-17.
  7. https://guardian.ng/news/kaduna-govt-sets-up-65-man-transition-committee-for-may-29-handover/