Giwa (Kaduna)

ƙaramar hukuma a Nigeria

An kirkiro ta ne a ranar 15 ga Satumbar 1991, da shugaban kasa na lokacin kuma babban kwamandan Tarayyar Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida GCFR, daga karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna. [2]

Giwa

Wuri
Map
 11°18′N 7°24′E / 11.3°N 7.4°E / 11.3; 7.4
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJihar Kaduna
Labarin ƙasa
Yawan fili 2,066 km²
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa supervisory councillors of Giwa local government (en) Fassara
Gangar majalisa Giwa legislative council (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Gari mai sunan Dabba
Asibitin giwa
  • tanbarin giwa
    Ƙaramar hukumar Giwa karamar hukuma ce a jihar Kaduna a Najeriya. Hedkwatar ta, tana cikin garin Giwa. Abubakar Lawal ne shugaban karamar hukumar Giwa Wanda yake kai a yanzu.[1]

Tana da yanki na 2,066 km2 da yawan jama'a 286,427 a ƙidayar 2006.

Tana da unguwanni 11 wadanda su ne shika, Idasu, Kadaga, Danmahawayi, Kidandan, Galadimawa, Gangara, Giwa, Kakangi, Pan Hauya da kuma yakawada kuma tare da kananan hukumomi 2 na cigaba.[2]

Tana nan a Arewa maso Yamma da Jihar Kaduna.[2] Lambar akwatin gidan waya na karamar hukumar Giwa ita ce 81 it0.[3][3][4]

An ƙirƙiro ta ne a ranar 15 ga Satumba 1991, a zamanin shugaban ƙasa na Mulkin Soja na, Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida GCFR, daga karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Tana da faɗin kasa Dayawa 2,066 km2 da yawan jama'a 2 a kidayar 2006. Tana da Gundumomi 11 su ne shika, Idasu, Kaɗage, Ɗanmahawayi, Kidandan, Galadimawa, Gangara, Giwa, Kakangi, Panhauya da kuma Yakawada kuma tare da mazaunin Ƴan Majalisar dokokin jihar Kaduna guda 2 Giwa ta Gabas Inda Tpl Adamu Muhammad Shika ke wakilta . da Giwa ta yamma wadda Hon.Umar Auwal Bajimi ke wakilta. Tana nan a Arewa maso Yamma a Najeriya

Lambar akwatin gidan waya na karamar hukumar Giwa ita ce 810.

Ayyukan Tattalin Arziki a Giwa

gyara sashe

Baban tattalin arzikin Al'ummar karamar hukumar Giwa shine Noma da kiwo da Ƴan Kasuwanni, sai ɗai_ɗai kun ma'aikatan Gwamnati.

Akwai kasuwannin mako-mako da ake ci a kasuwar Giwa . Kasuwar Galadimawa da Kasuwar Ɗa'a Wannan kasuwanni suna sayar da kayan gona da Dabbobi iri-iri.,

Jerin unguwanni a hukumar giwa

gyara sashe
  • Giwa
  • Danmahawayi
  • Idasu
  • Pan Hauya
  • Galadimawa
  • Kadage
  • Shika
  • Gangara
  • Kakangi
  • Kidandan
  • yakawada[5]

Manazarta.

gyara sashe