Latifa Lakhdar
Latifa Lakhdar (an haife tane a daya 1 ga watan Fabrairun shekarar alif dari tara da hamsin da shida miladiyya 1956) ta kasan ce masaniyar tarihi ne kuma Yar siyasa Yar kasar Tunusiya wacce ta kasance Ministan Al'adu daga Fabrairun shekarar 2015 har zuwa Janairun shekarar 2016.
Latifa Lakhdar | |||
---|---|---|---|
6 ga Faburairu, 2015 - 12 ga Janairu, 2016 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Zarzis (en) , 1 ga Faburairu, 1956 (68 shekaru) | ||
ƙasa |
French protectorate of Tunisia (en) Tunisiya | ||
Karatu | |||
Makaranta | College of Sorbonne (en) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Masanin tarihi, ɗan siyasa, Mai kare hakkin mata da marubuci | ||
Employers |
Ez-Zitouna University (en) Tunis University (en) |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Lakhdar a garin Zarzis a ranar 1 ga Fabrairun shekarar 1956. Ta kasance dalibar Mohamed Arkoun a Sorbonne a Faris.
Ayyuka
gyara sasheLakhdar ya kasance Farfesan Tarihin Zamani a Jami’ar Ez-Zitouna daga shekarata 1991 zuwa 1999 da kuma daga 2000 zuwa 2015 a Jami’ar Tunis .
Lakhdar gwani ne a cikin tunanin addinin musulunci kuma ya buga litattafai da dama cikin larabci da Faransanci, musamman kan yanayin mata a cikin al'ummomin Islama. Ita mace ce mai rajin kare hakkin mata da kuma bin addini . Ta yi iƙirarin cewa tsattsauran ra'ayin addinin Islama, gami da ta'addanci na Musulunci wani ɓangare ne na ƙa'idar addinin Islama, amma wannan tunanin na Islama zai iya zama mai haske da sassauƙa idan aka yi masa "juyin juya hali mai mahimmanci". Ta ce "Tunanin masu ra'ayin jihadi na cewa addini ya kamata ya mallaki siyasa, abin koyi ne da ba a taba samu ba."
Harkar siyasa
gyara sasheLakhdar memba ne na tunungiyar tunisienne des femmes démocrates . A shekarar 2011, an zabe ta a matsayin mataimakiyar shugaban babbar hukuma don tabbatar da manufofin juyin juya hali, Gyaran Siyasa da Canjin Dimokiradiyya .
A ranar 6 ga Fabrairu 2015, Lakhdar ya zama Ministan Al'adu da adana kayan tarihi, a matsayin mai zaman kansa, a gwamnatin Firayim Minista Habib Essid . Ta kasance tana tattaunawa da ma'aikatan gidan adana kayan tarihi yayin harin gidan kayan tarihi na kasa da kasa na Bardo a ranar 18 ga Maris Maris 2015 sannan daga baya ta bayyana abin tunawa a wurin.
A ranar 12 Fabrairu 2016, Lakhdar ya zama Kwamandan Umurnin Jamhuriya ta Shugaba Béji Caïd Essebsi don hidimarta.