Lambobin gidan waya a Najeriya lambobi ne da suka ƙunshi lambobi shida. NIPOST, Hukumar Kula da Gidan Wasiƙun Najeriya, ta raba ƙasar zuwa yan kuna tara, waɗanda ke zama lamba ta farko na lambar. Lambobin na biyu da na uku, haɗe da na farko, sune gundumar aikawa don rarrabawa. Lambobi uku na ƙarshe suna wakiltar wurin isarwa. Wurin isar da saƙo na iya zama kowane ɗayan waɗannan; wurin gidan waya, yankin karkara, ko yankin birni.

Lambobin gidan waya a Najeriya
aspect in a geographic region (en) Fassara
Bayanai
Facet of (en) Fassara lambar akwatun gidan waya
Ƙasa Najeriya

Babban ofishin gidan waya a kowane yanki zai kasance yanada lambar akwatin waya yana ƙarewa a 0001, don haka Garki Main HO a Abuja yana da lambar akwatin gidan waya 900001, Ikeja HO a Legas yana da 100001, Lokoja a Kogi yana da 270001, Port Harcourt yana da 500001. Mafi ƙarancin lambar gidan waya shine 100001 kuma mafi girma shine 982002. Bugu da kari akwai wasu lambobin waya na wasu jihohi a Najeriya, kamar yadda lambar gidan waya ta Enugu ita ce 400001, yayin da jihar Imo ke da 460001.

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe


Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe