Kwesi Akwansah Andam
Kwesi Akwansah Andam (15 Disamba 1946 - 14 Disamba 2007) malami ne ɗan ƙasar Ghana kuma tsohon Mataimakin Shugaban Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah.[1] Ya kasance farfesa a fannin Injiniyanci. Ya rasu a ranar 14 ga watan Disamba 2007 a Asibitin Soja na 37.
Kwesi Akwansah Andam | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 15 Disamba 1946 |
ƙasa | Ghana |
Mutuwa | 14 Disamba 2007 |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Aba Andam |
Karatu | |
Makaranta |
Ghana Senior High Technical School (Takoradi) (en) Kwame Nkrumah University of Science and Technology |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | Malami |
Kyaututtuka |
gani
|
Mamba | The World Academy of Sciences (en) |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Farfesa Andam a Ekumfi Atakwaa a tsakiyar ƙasar Ghana a ranar 15 ga watan Disamba 1946.[2] Ya samu takardar shaidar kammala karatunsa a makarantar sakandaren fasaha ta Ghana da ke Takoradi a yankin yammacin Ghana. Ya samu digirin farko na Kimiyya a fannin Injiniyanci a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah. Farfesa Andam ya sami digirin digirgir a fannin Injiniyancin Kwamfuta (CAD) a Jami'ar Newcastle, Newcastle a Tyne a Burtaniya.
Sana'a
gyara sasheA shekarar 1985, an naɗa shi malami a Sashen Injiniyanci na KNUST. Ya zama babban malami a shekarar 1985. Ya zama abokin farfesa a shekarar 1992 kuma cikakken farfesa a shekarar 1997.[1]
Mataimakin Shugaban KNUST
gyara sasheAn naɗa Andam a matsayin mataimakin shugaban jami’ar KNUST ta hukumar gudanarwar jami’ar.[1] Wa'adinsa na shekaru huɗu ya fara a watan Satumba na shekarar 2002 kuma ya ƙare a cikin watan Satumban 2006.[3]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheYa auri Farfesa Aba Andam wacce masaniya ce a fannin kimiyya kuma malama.[4] Sun haifi 'ya'ya huɗu.[5] Ya rasu a ranar 14 ga watan Disamba 2007 a Asibitin Sojoji na 37 bayan gajeriyar rashin lafiya.[1]
Wallafe-wallafe
gyara sasheAndam ya rubuta litattafai da takardu sama da 100 na kimiyya.[1]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 "Prof Kwesi Andam buried". www.modernghana.com. Archived from the original on 12 October 2012. Retrieved 20 July 2011.
- ↑ "Prof Kwesi Andam buried". www.ghanaweb.com. 30 November 2001. Archived from the original on 22 September 2011. Retrieved 20 July 2011.
- ↑ "Death of PROF. KWESI A. ANDAM". www2.aau.org. Archived from the original on 4 January 2011. Retrieved 20 July 2011.
- ↑ "Late Prof. Kwesi Andam Honoured". 5 November 2018. Archived from the original on 7 August 2019. Retrieved 7 August 2019.
- ↑ "Prof Kwesi Andam buried | General News 2008-03-01". 30 November 2001. Archived from the original on 7 August 2019. Retrieved 7 August 2019.