Ƙungiyar Noma ta Afirka ( French: Syndicat agricole africain, SAA) ita ce jam'iyyar siyasa ce ta farko a Cote d'Ivoire, karkashin jagorancin Félix Houphouët-Boigny har zuwa wa'adinta. An kafa ƙungiyar ne a ranar 3 ga Satumba 1944 wanda hanyar Houphouët-Boigny da gwamnatin mulkin mallaka suka kafa.

Kungiyar Noma ta Afirka
Bayanai
Iri jam'iyyar siyasa
Ƙasa French West Africa (en) Fassara
Tarihi
Ƙirƙira 1944
 
Felix Houphouët-Boigny

Houphouët-Boigny tare da gwamnatin mulkin mallaka suka kafa ƙungiyar a ranar 3 ga watan Satumban 1944 a wani taro a Abidjan. [1] A karkashin shugabancinsa, ta tattaro manoman Afirka wadanda ba su gamsu da albashinsu ba, suka kuma yi ƙoƙarin kare muradunsu daga na Turawa.[2][3] Masu adawa da mulkin mallaka da masu adawa da wariyar launin fata, ƙungiyar ta bukaci ingantattun yanayin ayyuka, Karin albashi, da kuma kawar da ayyukan bauta. [1] Kungiyar cikin gaggwa ta samu goyon bayan manoma kusan 20,000. [1] Nasarar ta ya harzuka turawan mulkin mallaka har suka ɗauki matakin hukunci kan Houphouët.[4] Duk da haka, kungiyar SAA ta ƙara shahara a matsayin muryar 'yan Afirka.[3]

Lokacin da aka zaɓe shi a majalisar wakilai a ranar 4 ga Nuwamba 1945, Houphouët-Boigny ya yi yinkurin cike burin SAA. Ya ba da shawarar daftarin doka don soke aikin tilastawa, tsarin mulkin Faransa ɗaya wanda ba shi da farin jini,[3] a ranar 1 ga Maris 1946 wanda Majalisar ta amince da shi a 1947.[5] On 9 April 1946,[6] A ranar 9 ga Afrilu 1946, [7] Houphouët-Boigny, tare da taimakon Groupes d'études communistes d'Abidjan, sun sake ƙirƙirar SAA a matsayin Jam'iyyar Democratic Party of Cote d'Ivoire (PDCI), jam'iyya ta farko mai tasiri a cikin Cote d'Ivoire[8] da sashen Ivory Coast na Rally Democratic Democratic Rally .

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 Ellenbogen, pp. 26–31.
  2. "Félix Houphouët-Boigny". Encyclopædia Universalis (in Faransanci). Paris: Encyclopædia Universalis. 1975.
  3. 3.0 3.1 3.2 Noble, Kenneth B. (1993-12-08). "Felix Houphouet-Boigny, Ivory Coast's Leader Since Freedom in 1960, Is Dead". The New York Times. Retrieved 2008-07-23.
  4. "Spécial Houphouet". Fraternité Matin (in Faransanci). Archived from the original on 2008-05-09. Retrieved 2008-07-22.
  5. "Biographies des députés de la IV République: Félix Houphouët-Boigny" (in Faransanci). National Assembly of France. Retrieved 2008-07-17.
  6. Toubabou, p. 60.
  7. Toubabou, p. 60.
  8. "Felix Houphouët-Boigny". Encyclopedia of World Biography. Thomson Gale. Retrieved 2008-07-25.

Bayanan kula

gyara sashe

Samfuri:Ivorian political parties